Jump to content

Patrick Aisowieren

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Patrick Aisowieren
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Orhionmwon/Uhunmwonde
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: Orhionmwon/Uhunmwonde
Rayuwa
Haihuwa 14 Oktoba 1972 (53 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Patrick Aisowieren ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya taɓa zama wakilin mazaɓar Orhionmwon/Uhumwonde a majalisar wakilan Najeriya a lokacin zaman majalisar wakilai ta 8 da ta 9. Siyasarsa ta fara ne a shekarar 2003 lokacin da aka zaɓe shi a matsayin kansila a ƙaramar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo. Daga nan ya ci gaba da zama ɗan majalisar dokokin jihar Edo mai wakiltar mazaɓar Orhionmwon ta gabas a shekarar 2007 da 2011, bi da bi. Ana kiransa da "Project Project."

[1] [2] [3] [4]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hon Patrick a ranar 14 ga watan Oktoba, 1972, ga dangin Aisowieren a ƙaramar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo, Najeriya. [5] [6] [3] Ya gama Makarantar Grammar Eweka da takardar shedar babbar makaranta. Ya ci gaba da karatunsa a Kwalejin Ilimi da ke Agbor, Jihar Edo, kuma ya sami takardar shaidar ilimin Najeriya (NCE) a shekarar 1997. Ya kammala karatunsa na digiri na farko a Jami'ar Jihar Delta a shekara ta 2001. [7]

An zaɓe shi ya zama kansila a jihar Edo a shekarar 2003. [1] Ya riƙe wannan muƙamin har zuwa zaɓensa a majalisar dokokin jihar Edo a shekarar 2007. [7] Ya kasance memba a majalisar daga shekarun 2007 zuwa 2011 da kuma daga 2011 zuwa 2015. [1] An zaɓi Hon Aisowieren ne a shekarar 2015 don wakiltar mazaɓar Orhionmwon/Uhunmwode a majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam'iyyar APC. A shekarar 2023 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi ɗan majalisar wakilai ta jihar Edo a hukumar NDDC

  1. 1 2 3 Nwafor (2022-01-12). "The enduring legacies of Hon. Patrick Aisowieren: Of quality representation, transformation in Orhionmwon/Uhunmwode Constituency". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-10-07. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":3" defined multiple times with different content
  2. Babah, Chinedu (2017-10-19). "AISOWIEREN, Hon Patrick". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2022-10-07.
  3. 1 2 "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2022-10-07. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  4. Daily Post Staff (2019-06-14). "What 9th National Assembly will do for Nigerians – Edo lawmaker, Aisowieren". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-10-07.
  5. "Public offices held by Patrick Aisowieren in Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2022-10-07.
  6. "ShineYourEye". www.shineyoureye.org. Retrieved 2022-10-07.
  7. 1 2 "Hon. Patrick Aisowieren biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-10-07. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content