Patrik Schick
Patrik Schick | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Prag, 24 ga Janairu, 1996 (28 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Kazech | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Yaren Czech | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 14 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 73 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 187 cm |
Patrik Schick (an haife shi a 24 ga watan Janairu shekarai 1996) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne mai buga gaba na qasar Czech republick wanda ke taka leda a matsayin mai gaba ga ƙungiyar Bundesliga Bayer Leverkusen da kuma ƙungiyar ƙasar ta Czech Republic .
Farkon rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shine a Prague, Schick ya fara aikinsa buga wasanni tare da qungiyar na gida Sparta Prague, yana tasowa ta hanyar matasan zaqaquransu su, kafin ya fara halarta na farko a matsayin matashi. A cikin shekarai 2016, yana da shekaru ashirin kacal 20, ya sami koma baya zuwa Sampdoria a qasar Italiya bayan da ya yi ban sha'awa tare da Bohemians a shekarai 1905 . Bayan kakar wasa ta farko mai ban sha'awa da qawatarwa a seria na qasar Italiya, ya koma Roma a cikin 2017 don ƙimar rikodin rikodin kulob din. A cikin 2019, Schick ya koma Jamus don shiga RB Leipzig a matsayin aro na tsawon lokaci kafin ya koma abokan hamayyar Bundesliga Bayer Leverkusen na dindindin a cikin Satumba 2020.
Sparta Prague ne ta hango dan wasan wanda aka haifaffen garin Prague ne lokacin yana yaro dan shekara sha daya 11. Ya yi wasansa na farko da Sparta a ranar uku 3 ga watan Mayu shekarar dubu biyu da shahudu 2014 a cikin rashin nasara dasukayi an dokesu daci uku da daya ci 3–1 a Teplice . Sparta za ta ci nasara sau biyu na wannan kamfen amma bayyanar hudu a kan kamfen biyu na nufin Schick ya ketare gari don shiga Bohemians 1905 akan aro don kakar 2015–16. [1] Ya zira kwallaye 8 a wasanni 27 na Bohemians a lokacin yakin faduwa. Schick ya koma Sparta kuma ana sa ran zai yi fice a kulob din a kakar wasa ta 2016-17, amma David Lafata ya fi so kuma lokacin da Sparta ta ba Schick sabon kwantiragi, wakilinsa ya ki amincewa. [2]
Schick ya saka hannu kan kwantiragin kan Sampdoria a watan Yuni shekarai dubu biyu da shashidda 2016 akan farashin kan yuro miliyan hudu na €4 miliyan. A kakar wasa ta farko a Italiya, ya bayyana a wasanni 32 na gasar kuma ya zira kwallaye 11 a Sampdoria. Ya fara sau 14 kuma ya sami damar samun bayan raga sau ɗaya a kowane minti 137. [3]
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Patrick Schick
-
Patrick a filin wasa
-
Patrick a gasar Euro ta shekarar 2020