Jump to content

Per mertesacker

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Per mertesacker
Rayuwa
Haihuwa Hanover, 29 Satumba 1984 (39 shekaru)
ƙasa Jamus
Ƴan uwa
Mahaifi Stefan Mertesacker
Abokiyar zama Ulrike Stange (en) Fassara  (2013 -
Karatu
Harsuna Jamusanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Germany national under-20 football team (en) Fassara2002-200320
  Hannover 962003-2006161
  Germany national under-21 football team (en) Fassara2003-200440
  Germany national association football team (en) Fassara2004-20141044
  SV Werder Bremen (en) Fassara2006-201114612
Arsenal FC2011-20181566
 
Muƙami ko ƙwarewa centre-back (en) Fassara
Mai buga baya
Tsayi 200 cm
Kyaututtuka
IMDb nm1851124
Per Mertesacker

Per Mertesacker An haife shi (29 ga watan September, 1984) ya kasance mai bada horo wato koci ga kasar jamus, sannan kuma dan wasa ne wanda yake buga baya. Kuma yanzu haka mai bada horo ne ko kuma koci a karamar kungiya ta Arsenal.

Mertesacker ya fara gudanar da rayuwar shi ta kwallo bayan ya samu ci gaba tun yana dan saurayi inda ya samu damar doka gasar Bundesliga a wata kungiya mai suna Hannover96, inda ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan wasa a shekarar alif dubu biyu da ukku 2003. Yana doka wurin baya ne a matsayin wurin da yake bugawa. Dan wasa ne mai natsuwa da kuma tarbiya sosai a cikin fili. Dan wasan ya buga wasanni 31 a lig ba tare da an fiddashi ba. Bayan namijin kokarin da yayi ma kungiyar tashi ta Hannover96 da kuma bajintar da yayi a kasarsa wato Jamus inda ya kasance yana cikin jerin yan wasan da suka buga gasar kofin duniya wadda akayiba shekarar alif dubu biyu da shida 2006 inda ya buga gasar yana dan shekara ashirin da daya 21. Yabar kungiyar ta Hannover96, inda ya doka wasanni har guda 74 a kungiyar a gasar lig, daga bisani kuma ya koma kungiyar kwallan kafa ta Werder Bremen akan jumillar kudi £5m. Zamaninshi a kungiyar Bremen din abun yabawa ne inda ya nuna jajircewa da kuma juriya ta hanyar tare farmaki da kuma sanya ma abokan wasanshi nutsuwa. Sakamakon hakan, ya samu babbar nasara a wannan kungiya inda ya samu nasarar lashe DFB Porkal tare da kungiyar tashi a shekarar alif dubu biyu da tara 2009. Sannan ya kare a cikin masu tsere na cin kofin UEFA Cup.

Bayan yabo da karbuwa dan wasan ya samu a gasar kofin duniya na shekarar 2010 sannan kuma kwantiragin sa ya kusa karewa, dan wasan ya matsa gaba inda yaje gasar Premier league inda ya kulla yarjejeniya da kungiyar Arsenal da jumillar kudi £8m. A kungiyar Arsenal, dan wasan ya shiga cikin mutum 11 na farko inda ake ganin yayi sa'a da kuma saurin shiga saboda yanayin girma da kuma kwararrun yan wasa da kungiyar keda su. Dan wasan ya shiga cikin manyan masu tsaron gida a kungiyar da kuma duniya ma baki daya. Ana yaban dan wasan akan kwanciyar hankali da nutsuwa da yake da ita. Dan wasan ya sanu kyakyawar alaka da abokin aikinsa wanda suke tsaron gida tare wato Laurent Kocielny inda auka samu jituwa a cikin filin wasa idan suna doka wasa inda suka shafe shekaru tara suna wasa tare kuma sun samu nasarar lashe gasanni da dama tare inda suna lashe kofin karshe a shekarar 2014 wanda suka buga da kungiyar Aston villa inda suka lallasa kungiyar Aston villa din daci 4-0 yayin da dan wasan ya samu damar jefa kwallo a raga.

Dan wasan ya zama captain na kungiyar Arsenal din saboda cancantar da yake da ita ta fannoni da dama. Daga bisani kuma ya dinga samun rauni ya dinga yawan yin jinya akai akai wanda hakan ne yasa a ajiye tamaula a shekarar 2018.

Salon wasa[gyara sashe | gyara masomin]

Mertesacker dan wasa ne mai tsayi inda tsawon sa yakai 1.98m (6 ft 6 in). Dan wasan ya kasance sarki ne a saman iska domin yana da tsayi kuma ya iya sama kwallo kai. Kuma yakanci kwallaye da kai kuma yana aci da kai. Kamar yadda yake sarki a sama, haka zalika a kasanma ba a baro shi a baya ba domin yana da basira ga kuma wayo da hikima da ze tare dan gaba kuma ya hana aci kwallo. Yana amfani da karfinsa domin ya anshi kwallo. Duk da cewa beda gudu sosai, amma yakan karanci wasa da kuma abokan hamayya domin ya kwaci kwallo daga hannunsu. Dan wasan be cika yi keta ba hakanan, yakanyi dubara ya kuma yi amfani da basira wajan ansar kwallo.

Mertesacker dan wasa ne mai basira kuma wanda yake natsar da kwallo domin da wadaci kowa. Anyi ittifakin cewa dan wasan yana daya daga cikin wadanda suke fin kowane dan wasa taba kwallo duk wasa.

Manzarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://en.wikipedia.org/wiki/Per_Mertesacker for 2017/18 Premier League confirmed". Premier League. 1 September 2017. Retrieved 8 September 2017.

"Per Mertesacker 'raps Ice Ice Baby' in delightful mash-up". Metro. 2 July 2014. Retrieved 17 December 2018