Prince Mpumelelo Dube (an haife shi a ranar 17 ga watan Fabrairu 1997) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Zimbabwe wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a kulob ɗin Azam FC da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe.[1][2]
A watan Agustan 2020, bayan shekaru da yawa yana wasa a ƙasarsa ta Zimbabwe, Dube ya koma ƙungiyar Azam ta Tanzaniya, inda ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku.[3]