Qaseim Suleimani
Qasem Soleimani ( An haife shi a ranar 11 ga watan Mayu a shekara ta 1957 – ya mutu a ranar 3 ga watan Janairu shekara ta 2020), kuma ana ce mai (Qassim Soleimani), ya kasance manjo janaral a kasar Iran a wata gidauniyar kasan mai suna Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) kuma tin daga a shekara ta 1998 har zuwa mutuwan shi ya kasance kwamandan rundunan Quds.
Soleimani ya fara aikin sojane tin a yakin Iran da Iraq a shekara ta 1980, wanda a lokacin yana umartan runduna na 41. An kashe Soleimani ne da wata jirgi mara mahayi, wacce ake sarrafa ta da na'ura, a ranar 3 ga watan Janairu shekarar 2020 a Bagadaza, wanda tsohan shugaban kasan Amurka Donal Trump ya rattaba hannu.
Abokiyar Zama
[gyara sashe | gyara masomin]Abokiyar zaman manjor janar Qasem soleimani sunan ta Zainab Soleimani.
Iyalan Sa
[gyara sashe | gyara masomin]Yakasance yanada yara kaman haka, Zainab soleimani, Sohrab Suleimani, Fatemah Suleimani, Muhammad Reza Suleimani, Ahmed Suleimani.