Rahoton Lafiya ta Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rahoton Lafiya ta Duniya
mujallar kimiyya
Bayanai
Farawa 1995
Laƙabi World Health Report
Muhimmin darasi global health (en) Fassara
Maɗabba'a Hukumar Lafiya ta Duniya
Ƙasa da aka fara Switzerland
Harshen aiki ko suna Turanci

Rahoton Lafiya ta Duniya ( WHR ) jerin rahotanni ne na shekara-shekara wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke fitarwa. An fara wallafa shi a shekarar1995, Rahoton Lafiya na Duniya shine wallafin WHO na kan gaba. [1] Ana wallafa rahotannin a kowacce shekara daga 1995 zuwa 2008, sannan kuma a cikin 2010 da 2013. Ana samun rahotannin a cikin yaruka da dama, kuma suna samun tantance daga ƙwararru akan wani takamaiman batun kiwon lafiya na duniya, wanda ya shafi dukkannin ƙasashen da suke membobin ƙungiyar. [2]

Babban manufar WHR ita ce samar da muhimmman bayanai ga masu tsara manufofi, hukumomin ba da agaji, kungiyoyin kasa da kasa da sauran su don taimaka musu wajen yanke manufofin kiwon lafiya da suka dace da kuma yanke shawara akan tallafi. Duk da haka, rahoton kuma yana samun isa ga mafi yawan masu sauraro, kamar jami'o'i, 'yan jarida da sauran jama'a. Ana sa ran cewa duk wani ƙwararre ko kuma wanda ke da ra'ayi akan amuran kiwon lafiya na duniya, zai iya karantawa kuma yayi amfani da shi.

Jerin jigogi dangane da shekara[gyara sashe | gyara masomin]

Kowane WHR tana magance jigo daban-daban. A kasa akwai jerin rahotanni da jigogi.

  • 2013: Research for universal health coverage
  • 2010: Health systems financing: The path to universal coverage
  • 2008: Primary health care: Now more than ever
  • 2007: A safer future: global public health security in the 21st century
  • 2006: Working together for health
  • 2005: Make every mother and child count
  • 2004: Changing history
  • 2003: Shaping the future

  • 2002: Reducing risks, promoting healthy life
  • 2001: Mental health: new understanding, new hope
  • 2000: Health systems: improving performance
  • 1999: Making a difference
  • 1998: Life in the 21st century: a vision for all
  • 1997: Conquering suffering, enriching humanity
  • 1996: Fighting disease, fostering development
  • 1995: Bridging the gaps

WHR 2013: Bincike don ɗaukar nauyin lafiya na duniya[gyara sashe | gyara masomin]

Rahoton Lafiya na Duniya na 2013 ta mai da hankali kan mahimmancin bincike don haɓaka ci gaba zuwa ɗaukar nauyin kula da lafiya na duniya - a wasu kalmomi, cikakken damar yin amfani da ayyuka masu inganci don rigakafi, jiyya da kariyar haɗarin asarar dukiya. Rahoton yana ba da shawarar kara zuba jari na kasa da kasa da na kasa a cikin bincike da nufin inganta ayyukan kiwon lafiya a ciki da tsakanin kasashe. [3] Misalan binciken da ake buƙata sun haɗa da binciken magunguna, ko bincikar abubuwan da ke haifar da rashin lafiya da kuma abubuwan da ake bukata don inganta kiwon lafiya da jin dadi, da kuma bincike na ayyukan kiwon lafiya, mayar da hankali kan yadda za a fadada ayyukan da kuma rage rashin daidaito a wajen dakan nauyi

Rahotannin da suka gabata[gyara sashe | gyara masomin]

2010: Tallafin Tsarin Kiwon Lafiya[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2010 ta mayar da hankali ne akan kula da kiwon lafiya na duniya, da kuma yadda kasashe zasu canza tsarin tallafin kudadensu don cimma wannan buri. Rahoton ya samar da ajenda na matakai ga kasashe daga kowanne mataki na cigaba, kuma ta bada shawara akan yadda kasashen duniya zasu tallafawa manufofi a kasashe da ke da karamin karfi don cimma nasarorin shiga tsarin kiwon lafiya ta duniya da kuma bunkasa sakamakon kiwon lafiyar jama'a.[4]

2008: Kiwon lafiyar ta farko[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2008 ya ta'allaka akan sabunta kiwon lafiya ta farko, da kuma bukatar Tsarin Lafiya da ta inganta mayar da martani acikin sauri ga matsalolin kiwon lafiya a wannan duniya mai canzawa.[5]

2007: Tsaron kiwon lafiyar jama'ar duniya[gyara sashe | gyara masomin]

Muhimmin kudurin Rahon Lafiya ta Duniya ta 2007 sun ta'allaka akan cewa, duka duniya na cikin barazanar barkewar cututttuka, annoba, hadurran masana'antu, tashin hankali na yau da kullum da kuma sauran tashe-tashen hankula wadanda ka iya zama barazana ga tsaron lafiyar jama'a. Rahoton ya nuna yadda sabbin Dokokin Lafiya na Kasa da Kasa ke taimakawa kasashe wajen aiki tare wajen gano hadurra da kuma daukan matakai na tsayar da su da kuma sarrafa su.[6]

2006: Aiki tare don kiwon lafiya[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2006 (WHR2006), ta bayyana karancin ma'aikatan lafiya akalla miliyan 4.3, da suka hada da likitoci, ma'aikatan jinya, unguwannin zoma da sauran maikatan kiwon lafiyaa fadin duniya, kuma suka kira yanayin da "matsalolin ma'aikatan lafiya na duniya". Rahoton ya shimfida tsarin matakai na tsawon shekaru goma don gina ma'aikatan kiwon lafiya a tsakanin kasashe ta hanyar horarwa na musamman, daukar ma'aikata da kuma hanyoyin sarrafa su.[7]

2005: Kiyaye kowacce mahaifiya da dan ta[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2005 ya mayar da hankali akan cewa akalla yara miliyan 11 'yan kasa da shekaru biyar suna mutuwa daga ciwuka wadanda za'a iya magance su, sannan kuma akalla mata 500 na mutuwa a wajen rainon ciki, wajen haihuwa, ko kuma da zarar an haihu. Rahoton ya bayyana cewa, rage wannan mace-mace dangane da tsarin Millennium Development Goals zai ta'allaka ne akan kowacce mahaifiya da kuma kowanne yaro da su samu damar hakkin kiwon lafiya tun daga daukan ciki har zuwa haihuwa, da rainon jariri har zuwa yarintarsa.[8]

2004: Canza tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Batun Rahon Lafiya ta Duniya ta 2004 ya kasance akan annobar HIV/AIDS a fadin duniya.[9]

2003: Tsara gaba[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2003 ya auna yanayin lafiya ta duniya da kuma wasu muhimman barazana ga lafiya. Rahoton ya bayyana cewa an kusa samu muhimmin cigaba a cikin shirin lafiya ga kowa, sannan kuma cigaba ya ta'allaka ne akan hadin gwiwa a tsakanin gwamnatoci, cibiyoyin kasa da kasa, ma'aikatu masu zaman kansu, da kuma kungiyoyin 'yan kasa don gina tsarin kiwon lafiya masu inganci.

2002: Rage hadurra, bunkasa ingantacciyar rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2002 ta bayyana dumbin cututtuka, tawaya, da mace-mace a duniya da ke da alaka da wasu muhimman abubuwa masu hatsari ga rayuwar dan-adam. Ta bayyana yadda za'a iya rage wannan nauyi a cikin shekaru 20 masu zuwa idan an rage wadannan abubuwa masu hatsari.

2001: Matsalolin lafiyar kwakwalwa[gyara sashe | gyara masomin]

An mayar da hankali akan watsi da matsalolin kwakwalwa a cikin Rahon Lafiya ta Duniya ta 2001. Rahoton ta fitar da awon ayyukan tsarin lafiya na kasa na kowacce kasa.

2000: Tsare-tsaren lafiya: inganta lafiya[gyara sashe | gyara masomin]

Rahon Lafiya ta Duniya ta 2000 ta gabatar da wasu tsare-tsare da hanyoyin gwaje-gwaje wajen aunawa da danganta harkokin tsarin lafiya a fadin duniya, da kuma yadda za'a fi fahimtar rikitattun abubuwan da suke bayyana yadda tsarin lafiya ke wakana.[10] Rahoton ta fitar da awon ayyukan tsarin lafiya na kasa na kowacce kasa.

Kara bincike[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin hadin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. World Health Organization: Publications
  2. World Health Organization: Alphabetical List of WHO Member States
  3. World Health Organization: Main messages from World health report 2013: Research for universal health coverage. Last update 19 August 2013. Accessed 26 August 2013.
  4. World Health Organization: The world health report 2010 - Health systems financing: the path to universal coverage
  5. World Health Organization: The World Health Report 2008 - Primary Health Care (Now More Than Ever)
  6. World Health Organization: The world health report 2007 - A safer future: global public health security in the 21st century
  7. World Health Organization: The World Health Report 2006 - working together for health
  8. World Health Organization: The World Health Report 2005 - make every mother and child count
  9. World Health Organization: The world health report 2004 - changing history
  10. World Health Organization: The world health report 2000 - Health systems: improving performance."