Rakiya Musa
'Rakiya Musa jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood tayi suna ta shahara ta ɗaukaka, tayi fina finai da dama a masana'antar, tana Hawa Waƙoƙin soyayyah tayi suna a wannan fannin tana Hawa Waka da Hamisu Breaker, Auta MG Boy, Garzali Miko [1]da sauran su.[2]
Takaitaccen Tarihin Ta
[gyara sashe | gyara masomin]Rakiya Musa haifaffiyar ƙasar nijar ce kyakkyawar mace acikin yammatan kannywood. Iyayenta Yan ƙasar nijar ne Amma sun haifeta a garin Lagos a ranar 2 ga watan nuwamba, tayi karatun firamare da sakandiri har zuwa makarantar gaba da sakandiri duka a garin Lagos. mutane da dama sunfi sanin ta suna Aisha humaira, sanadiyyar fim din da tayi da jarumi Adamu zango shine ya haskaka [3]ta a masana'antar .
Masana'antar fim
[gyara sashe | gyara masomin]Jaruma Rakiya ta shigo masana'antar fim a shekarar 2011 ta hanyar jarumi Adamu zango tayi fi. Din ta na farko Mai suna Aisha humaira SE fim ɗin daren alkhairi, tayi fina finai da dama a masana'antar.[4]
Fina finan ta;
- Yar agadez
- Aisha humaira
- Daren alkhairi
- basaja
- Yau da gobe
- Attajiri
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.