Jump to content

Rashid Seidu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rashid Seidu
Rayuwa
Haihuwa Accra, 14 Satumba 1995 (29 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Asante Kotoko F.C. (en) Fassara-
 

Rashid Seidu (an haife shi a ranar 14 ga watan Satumban 1995) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne, ɗan ƙasar Ghana wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida. A cikin shekarar 2015, ya sami kira na ƙasa kuma ya kasance memba na Ghana U23 a 2015 All-Africa Games. [1]

Aikin kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

Seidu ya rattaba hannu a ƙungiyar ƙwararru ta Asante Kotoko, a ranar 3 ga watan Janairun 2011. Kuma ya koma kulob ɗin AS Douanes na Nijar (Niger) inda ya ƙulla kwantiragi na shekara tare da zaɓin sabunta shi a ƙarshen kakar wasa ta bana amma ya ɗan yi jinkiri[2].

Daga bisani ya koma Bechem United a cikin watan Yulin 2013, inda ya rattaɓa hannu kan shekaru biyu da kulob ɗin gasar Premier ta Ghana[3][4].

A cikin shekarar 2015, Seidu ya koma kulob ɗin gasar Premier ta Ghana Wa All Stars yanzu Legon Cities kan yarjejeniyar shekaru huɗu. A cikin watan Mayun 2020, ya shiga Inter Allies.

Ayyukan ƙasa da ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Janairun 2015 an gayyace shi don shiga cikin tawagar ƙasa ta U23 a wasannin share fage na Wasannin Afirka duka.

Asante Kotoko

  • Gana Premier League: 2011-2012

Bechem United

Wa All Stars

  • Gana Premier League: 2016
  • Gana Super Cup: 2017

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Rashid Seidu at FootballDatabase.eu