Rawani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
rawani
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na headgear (en) Fassara

Rawani Yana daga cikin sutura da Hausawa suke amfani da ita kuma suke girmamawa. Sai dai kuma ba duk bahaushe yake amfani da rawani ba, a ƙasar Hausa idan kaga mutum da rawani to cikin waɗannan mutanen ne, Sarki, ɗan Sarki ko kuma wanda yake da alaƙa da sarauta, ko kuma yanada wata sarautar daban. Ɓangarenangaren sarauta kenan, idan kuma muka dawo ɓangaren Malunta misali idan kaga Mutum da rawani to kodai Malami ko Almuhajir (Almajiri). Sai kuma ɓangaren tsofaffi suma ba'a barsu a baya ba don suma sukanyi amfani da rawani sosai. Wannan shine rukunin mutane uku (3) masu amfani da rawani a ƙasar (Hausa) sai dai akwai ƴan kaɗan masu ra'ayin sa rawani suma suna sashi. Amma waɗancan rukunin uku sune asali aka sani da rawani. Sai dai rawanin Malamai daban, haka na sarakuna daban, haka tsofaffi shima daban. Rawanin sarakuna shine yafi ko wane rawani girma don nasu har mai ƙaho biyu akwai. Sai rawanin Malamai shima yana biye da na Sarakuna, sai na tsofaffi shikam wani lokacin ma zaka gashi dai wani daƙun-daƙun dashi. A taƙaice Rawani wata sutura ce da ake ado da ita a ƙasar Hausa wadda mafi yawanci mutum ukun na kasa sunfi amfani da ita. .Sarki .Malamai .Tsofaffi[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-06-11. Retrieved 2021-06-11.