Robert Allan, Baron Allan of Kilmahew
Robert Alexander Allan, Baron Allan na Kilmahew, DSO , OBE , RD (11 Yuli 1914 - 4 Afrilu 1979) ɗan siyasa ne naConservative dake Biritaniya.
Allan ya yi karatu a Makarantar Harrow, Kwalejin Clare, Cambridge da Jami'ar Yale.[1] Ya yi aiki darundunar Royal Naval Volunteer Reserve l a lokacin Yaƙin Duniya na II kuma an nada shi jami'i na Order of the British Empire (OBE) a shekara ta 1942, Ma'abocin mukain Distinguished Service Order (DSO) a cikin 1944, [2] kuma an ba shi kyautar Faransa Croix de guerre . [3]
Allan ya kasance ɗan majalisa (MP) a mazaɓar Paddington South tsakanin 1951 zuwa 1966. A cikin 1958 da 1959, ya kuma kasance Sakataren Kuɗi na Admiralty.
A ranar 16 ga watan Yulin 1973, an bashi matsayin Baron Allan na Kilmahew, na Cardross a cikin gundumar Dunbartonshire . [4]
Ɗansa Sir Alex Allan ya kasance tsohon babban ma'aikacin gwamnati, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin haɗin gwiwar leƙen asiri na Joint Intelligence Committee.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ ALLAN OF KILMAHEW, Baron (Robert Alexander Allan)". Who's Who. ukwhoswho.com. Vol. 2021 (online ed.). A & C Black, an imprint of Bloomsbury Publishing plc. (Subscription or UK public library membership required.)
- ↑ "No. 36697". The London Gazette (Supplement). 12 September 1944. p. 4217.
- ↑ "No. 37338". The London Gazette (Supplement). 6 November 1945. p. 5401.
- ↑ "No. 46031". The London Gazette. 19 July 1973. p. 8403.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Hansard 1803–2005: contributions in Parliament by Robert Allan
Unrecognised parameter | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |