Jump to content

Saliu Mustapha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saliu Mustapha
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
District: Kwara central
Rayuwa
Haihuwa Kwara, 1973 (50/51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Saliu Mustapha
Da kwara state ne

Saliu Mustapha dan siyasan Najeriya ne kuma dan jam’iyyar All Progressives Congress. Ya kasance mataimakin shugaban Congress for Progressive Change, daya daga cikin rusassun jam’iyyun siyasa da suka hade suka kafa All Progressives Congress.[1][2][3]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mustapha a ranar 25 ga watan Satumban, shekarar alif dari tara da saba'in da biyu miladiyya 1972 a jihar Ilorin, jihar Kwara. Ya halarci makarantar firamare ta Bartholomew da ke Zariya don karatunsa na firamare sannan ya zarce zuwa Makarantar Sakandare ta Command da ke Kaduna don karatunsa na sakandare. Yayi karatun injiniyan albarkatun kasa a kwalejin fasaha dake a jihar Kaduna.

Harkar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rayuwar siyasar Mustapha ta fara ne a farkon karni na 21 lokacin da ya zama sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar Progressive Action Congress (PAC), rusasshiyar jam'iyyar siyasa da ta yi takara a zaben shugaban kasar Najeriya na shekarar 2003 . Ya kuma zama memba na ANPP kuma ya dukufa ga burin shugaban kasa na Muhammadu Buhari . A shekara ta 2009, lokacin da wani bangare na jam’iyyar ANPP da ke karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ya kafa Congress for Progressive Change, Mustapha ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar. Ya rike wannan mukamin har sai da jam’iyyar ta hade ta kuma kafa jam’iyyar All Progressives Congress .[4][5][6][7][8][9]

Zaben fidda gwani na jihar Kwara a shekara ta 2018

[gyara sashe | gyara masomin]

Mustapha ya tsaya takara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na jihar Kwara a shekara ta 2018 kuma ya samu goyon bayan yankin arewacin jihar. Ba shi da damar shiga tsakiyar zaben. Kwamitin Aiki na Kasa daga baya ya nemi afuwa kan dakatar da shi.

Tallafawa matasa da ci gaban al'umma

[gyara sashe | gyara masomin]

Mustapha yana da gidauniya a garin sa na sadaukar da kai domin taimakawa matasa. A cikin shekara ta 2019 da shekara ta 2020, kuniyar ta bayar da fom din JAMB na shekara ta 2000 kyauta ga daliban da aka zaba.

  1. "Mustapha, former CPC leader joins APC chairmanship race". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2021-04-18. Retrieved 2021-04-19.
  2. editor (2021-03-21). "APC Chairmanship: Who Are the Candidates?". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2021-04-19.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  3. "Update: ACN, ANPP, APGA, CPC merge into new party, APC - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2013-02-07. Retrieved 2021-04-19.
  4. "Elections in Nigeria". africanelections.tripod.com. Retrieved 2021-04-19.
  5. editor (2021-04-12). "Can Young Saliu Mustapha Make a Difference as APC National Chairman?". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2021-04-19.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  6. Okocha, Chuks (2021-04-15). "Nigeria: 'I Have Been Brought Up Under Buhari's Political Tutelage '". allAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2021-04-19.
  7. "Ilorin Emirate backs Mustapha's APC Nat'l Chairmanship bid | The Nation". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2021-04-16. Retrieved 2021-04-19.
  8. "Lying politicians responsible for insecurity, ethnic agitations in Nigeria - APC chieftain" (in Turanci). 2021-04-06. Retrieved 2021-04-19.
  9. "CPC stakeholders' meeting ends in chaos". Vanguard News (in Turanci). 2011-05-06. Retrieved 2021-04-19.