Jump to content

Sallah Azzahar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sallah Azzahar
Sallah
Bayanai
Mabiyi Sallan Alfijiri
Ta biyo baya Sallar la`asar
Dattijon Musulmi lokacin Sallar Zuhur a Masallacin Jama

Sallar Zuhur ( Larabci: صَلَاة ٱلظُّهْر‎ ) tana ɗaya daga cikin sallolin Musulunci na farilla ( sallah ). Ana yin ta ne bayan sallar asuba da kuma gabanin sallar la'asar, tsakanin gushewar rana daga tsakiya shine zaɓaɓɓen lokacin ta zuwa kusa da lokacin La'asar tana zamowa laluri ne zuwa faɗuwar rana.[1]

A ranar Juma’a ana maye gurbin Sallar Azahar da sallar Juma’a wadda wajibi ce ga maza Musulmi waɗanda suka wuce shekarun balaga kuma suke baligai masu hankali da lafiya su yi salla a cikin jam’i ko dai a masallacin Jumu'a ko kuma dai ga waɗanda basu samu sallar juma'a ba, Sai suyi Sallah Azahar raka'a huɗu kenan cif.[ ]

Khutbah (wa'azi) liman ne yake gabatar da ta, a ranar juma'a.

Kuma ana kiranta da Zuhr, Duhr, Thuhr ko Luhar.

Salloli biyar a dunkule guda ɗaya ne na rukunnan Musulunci guda biyar, a cikin Musuluncin Sunna, kuma ɗaya daga cikin rukunan Imani.

  1. "Sunan Abi Dawud 1067 - Prayer (Kitab Al-Salat) - كتاب الصلاة - Sunnah.com - Sayings and Teachings of Prophet Muhammad (صلى الله عليه و سلم)". sunnah.com. Retrieved 2023-05-08.