Jump to content

Sarauniya Mangou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sarauniya Mangou
noble title (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Nijar
Wuri
Map
 13°51′28″N 4°14′34″E / 13.8578°N 4.2428°E / 13.8578; 4.2428

Sarauniya Mangu ita ce sarauniyar da ta yi sarauta a kan Aznawa da ke yankin Dogon Doutchi a Nijar. Ta yi mulki ne a ƙarshen karni na 19 a Kudu Maso Yammacin kasar Nijar ta yanzu a cikin Afirka ta Yamma. Sarauniya ba Shi ne taken da ake mata ba domin zamanta jagorar siyasa da addini a garin Lugu,[1] wanda yake tsawon kilomita ashirin daga garin Matankari. A cewar bayanai da aka tattara dangane da Sarauniya, asalin sunanta Mangu [2] (ko Mangou da turancin Faransa).

Ana tuna ta ne saboda jarumtar da ta gwada ita da al'ummarta wajen yakar 'Voulet-Chanoine'. ; a lokacin da daulolin yankin Afirka ta Yamma da yawa suka mika wuya ga mamayar Faransa ba tare da yin wani yaƙi ba. Al'ummar Sarauniyan sun yaƙi sojojin mulkin mallaka waɗanda Kyaftin 'Voulet da Chanoine' suka jagoranta a cikin watan Afrilun shekarar 1899.

Tarihin Rayuwarta

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanan tarihin da suka shafi Sarauniyan ba su da yawa, kuma galibi suna da alaƙa da gwagwarmaya da 'Voulet-Chanoine'. an kuma haɗa su da abubuwan almara daga al'adun gatan Afirka. An kuma rawaito abinda ya faru tsakanin fitattun mayaƙan Aznas da ginshiƙin da Kyaftin 'Voulet da Chanoine' suka jagoranta a cikin littafin da aka buga a cikin adanannun rubuce-rubuce da ɗaya daga cikin membobin wadannan sojojin Faransar wato Janar Joalland (Laftana a lokacin). Wannan sojan ya suffanta Sarauniya Mangu a matsayin wata tsohuwar matsafiya wadda ta yi musu barazanar tare wa Faransa hanya domin ganin Faransawa sun iso kusan garin nata, inda kuma ta tura musu da sakon cin mutunci da cewar ta yi alkawarin ba za ta bari su wuce ba; tare da nuna kasaitar mayakanta. A ranar 16 ga watan Afrilu, sojojin Faransa sun kusa isa shigar garin Lugu, inda mayaƙan Sarauniya suka fuskance su. A cewar acancen rubutun Joalland, Faransawa sun tarwatsa abokan hamayyarsu ba tare da wahala da wasu yan bindigogi kadan. Duk da haka, an tilasta wa sojojin Faransa yin yaƙi daga baya don su fatattaki 'mahalba da ke cikin daji inda suka samu mafaka, saboda sojojin Faransa sun yi zango a kusa. Sakamakon turjewar mayaƙan garin Lugu, al'amarin ya zama babbar asara ga Faransawan, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu, da raunuka shida da kuma asarar kusan harsashe dubu bakwai (7 000) [3].

Aznas sun nemi mafaka a cikin daji, 'yan makonnin baya haka, bayan tafiyar Faransawa, sun sake mallakar garin Lugu [1], wanda sojojin mulkin mallaka suka ƙone kurmus. A cewar bayanan da aka samo, mayakan Sarauniya sun tafi da ita da karfi a lokacin yakin. A cewar labaran da ke yawo, Mangu ta yi yunƙurin kashe kanta ta hanyar jefa kanta cikin wuta, domin tsananin bakin-cikin rashin samun nasarar kare ƙabilarta, to sai dai an hanata yin hakan. Rahotanni sun nuna cewar bayan mutuwarta, wata itaciyar magarya ta tsiro saman kabarinta abinda a cewar wasu ke nuna rashin mutuwarta [2].

Sabanin Labarai

[gyara sashe | gyara masomin]

Taskar labarai na Ma'aikatar Yaki ta Faransa ta nuna cewar mazauna garin Lugu sun nuna turjiya ga sojojin Faransa amma ba a ambaci rawar ganin da Sarauniya Mangu ta taka ba. Galibi al'adun gargajiyar ne suka sanya Sarauniyar shahara a wasu yankuna na ƙasar ta Nijar, suna martabar da ita saboda adawa da Faransa da kuma sihiri da ta iya. An sake ambaton Yaƙin Lugu a wani nassi daga littafin Le Grand capitaine (1976), labarin almara wanda 'Jacques-Francis Rolland' ya ba da shi kan ayyukan 'Voulet-Chanoine; marubucin ya gabatar da Sarauniya a matsayin wata "Sarauniyar-tsafi" wadda ke anfani da tsafi wajen jagorantar mayakanta da kuma sanya tsoro a cikin zuciyar sojojin Faransa. To sai dai Sarauniya Mangu tayi suna ne musamman daga shekarar 1980 sanadiyyar wani marubucin Nijar mai suna Mamani Abdoulaye wanda ya rubuta littafi sukutum(Sarraounia: Le drame de la reine magicienne) kan Sarauniya wadda tarinta yakasance wata almara da batada tabbas [1] .

Mamami — wanda ya ce ya yanke shawarar rubuta littafin nasa a matsayin martani ga 'Rolland', wanda ya kasance kamar raini a gare shi  alamomi da gangan labari, An yi niyyar ba da tarihin Afirka na tarihin mulkin mallaka. Yayinda Joalland, mai shaida akan taron, yayi magana akan Sarauniya a matsayin tsohuwar mayya, Mamani ya bayyana ta a matsayin budurwa kuma kyakkyawar mace, kwatankwacin babban jarumin Amazon. ya sanya ma ta wata alama ta siyasa, yana ba ta jawabi tare da lafazin nuna wariyar launin fata. Adadin Sarauniya, wanda yake daɗaɗawa ta wannan labarin da aka kirkira, ya zama na baya-baya alama ce ta yaƙi da mulkin mallaka [4] .

Ba a santa da yawa ba kafin shekarar 1980, ta zama, bisa ga sake shigar da adabi, wata alama ce ta alfarmar Afirka da juriya ta ƙasa, kuma daga baya ta shiga cikin littattafan makaranta a cikin Faransanci - mai magana da yaran Afirka [2] , [1]. Daga cikin wasu abubuwan, ita ce jarumar fim din da ta dace daga littafin Mamani, wanda (Med Hondo) ya jagoranta, kuma ta fito a cikin ayyukan kirkirarrun labarai.

Nassoshi da Aka Buga

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Paul Joalland (général), Le Drame de Dankori : mission Voulet-Chanoine - mission Joalland-Meynier, Paris, Nouvelles Éditions Argo (NEA), 1930, 256 p.

Gajerun Rubuce-Rubuce

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Elara Bertho, « Sarraounia, une reine africaine entre histoire et mythe littéraire (Niger, 1899-2010) », Genre & Histoire [En ligne], 8 | Printemps 2011, mis en ligne le Samfuri:Date-, consulté le Samfuri:Date-. URL : http://genrehistoire.revues.org/1218
  • Aissata Sidikou, « De l'oralité au roman : Sarraounia ou la reine contre l'empire », The Romanic Review, vol. 93, n° 4, Samfuri:Date-.
  • Antoinette Tidjani Alou, « Sarraounia et ses intertextes : Identité, intertextualité et émergence littéraire », Sud Langues, revue électronique internationale des sciences du langage, n° 5, http://www.sudlangues.sn/spip.php?article91 Archived 2021-04-21 at the Wayback Machine
  • Ousamane Tandina, « Sarraounia an epic ? », Research in African Literature, vol. 24, n° 2, 1993, p. 13-23.
  • Denise Brahimi et Anne Trevarthen, préf. de Catherine Coquery-Vidrovitch, Les femmes dans la littérature africaine : portraits, Paris / Abidjan / Paris, Karthala / Centre d'édition et de diffusion africaines (CEDA) / Agence de la Francophonie-ACCT, 1998, 238 p., 08033994793.ABA (Karthala) - 08033994793.ABA (CEDA)
  • Samfuri:Ouvrage.
  • Nicole Moulin, Boubé Namaïwa, Marie-Françoise Roy, Bori Zamo, Lougou et Saraouniya, Paris, L'Harmattan - Tarbiyya Tatali, 2017, 232 p., 08033994793.ABA.
  • Samfuri:Ouvrage, Samfuri:Lire en ligne.


  • Abdoulaye Mamani, Sarraounia : Le drame de la reine magicienne, L'Harmattan, coll. « Encres Noires », 1989, 160 p., 08033994793.ABA (première édition : 1980).
  • Samfuri:Ouvrage.
  • Halima Hamdane (scénario), Isabelle Calin (dessin), Sarraounia : la reine magicienne du Niger, Paris, Cauris, collection « Lucy », 2004, 24 p., 08033994793.ABA (livre pour enfants)

Hoton Bidiyo na zane

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Christophe Dabitch (scénario) et Nicolas Dumontheuil (dessins et couleurs), La Colonne, t. 1 : Un esprit blanc, Paris, Futuropolis, 2013, 77 p. (ISBN 978-2-7548-0712-8, présentation en ligne).
  • Christophe Dabitch (scénario) et Nicolas Dumontheuil (dessins et couleurs), La Colonne, t. 2 : Exterminez-moi toutes ces brutes, Paris, Futuropolis, 2014, 87 p. (ISBN 978-2-7548-0887-3, présentation en ligne).
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Sarraounia, une reine africaine entre histoire et mythe littéraire (Niger, 1899-2010), Genre et histoire, printemps 2011
  2. 2.0 2.1 2.2 Odile Goerg et Anna Pondopoulo (dir), Islam et sociétés en Afrique subsaharienne à l'épreuve de l'histoire, Karthala, 2012, pages 157-171
  3. Général Joalland, Le drame de Dankori, Argo, 1930, page 58-59
  4. Antoinette Tidjani Alou, Sarraounia et ses intertextes Archived 2007-07-03 at the Wayback Machine, Revue électronique internationale de sciences du langage, 2001