Shaaban Idd Chilunda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shaaban Idd Chilunda
Rayuwa
Haihuwa Tandahimba District (en) Fassara, 20 ga Yuni, 1998 (25 shekaru)
ƙasa Tanzaniya
Harshen uwa Harshen Swahili
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Swahili
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
C.D. Tenerife (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka

Shaaban Idd Chilunda (an haife shi a ranar 20 ga watan Yuni 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Tanzaniya wanda ke taka leda a kulob din Moroccan Moghreb Tétouan a matsayin ɗan wasan gaba.

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Tandahimba, Chilunda ya shiga tsarin matasa na Azam FC a 2012. Ya buga wasansa na farko a cikin shekarar 2016, kuma a ranar 9 ga watan Yuli 2018, ya zira kwallaye hudu a wasan da suka doke Rayo Sports FC da ci 4-2 a gasar cin kofin Kagame Interclub na shekara;[1] ya kuma zura kwallon farko a wasan karshe da suka doke Simba SC da ci 2–1.[2]

A ranar 7 ga watan Agusta 2018, Chilunda ya amince da yarjejeniyar lamuni na shekaru biyu tare da Sifen Segunda División CD Tenerife, bayan lokacin gwaji.[3] Ya buga wasansa na farko na ƙwararru bayan kwanaki goma sha uku, yana zuwa a matsayin wanda zai maye gurbin Filip Malbašić a wasan da suka tashi 1-1 da Gimnàstic de Tarragona.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Cecafa Kagame Cup 2018: Four Star Shabani Idi propels holders Azam fc to the semi finals" . MySoccer24.com. 9 July 2018. Retrieved 13 August 2018.
  2. "Azam beat Simba to retain Kagame Cup as Gor wins bronze medal" . The Standard Media. 13 July 2018. Retrieved 13 August 2018.
  3. "Shaban Idd Chilunda, nuevo refuerzo del CD Tenerife" [Shaban Idd Chilunda, new addition of CD Tenerife] (in Spanish). CD Tenerife. 7 August 2018. Retrieved 13 August 2018.
  4. "Aveldaño acude al rescate del Tenerife en el 93' " [Aveldaño comes to the rescue of Tenerife in the 93'] (in Spanish). Marca . 20 August 2018. Retrieved 21 August 2018.