Shah
Appearance
Shah | |
---|---|
noble title (en) da historical position (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | ruler (en) da sultan (en) |
Ƙasa | Daular Safawiyya |
Shah ( Persian ) kalma ce ta Fasha wacce ke nufin sarki ko mai mulkin wata ƙasa. Ana amfani da wannan kalmar a ƙasashe daban-daban na duniya, ciki har da Iran, Indiya, Pakistan da Afghanistan . A halin yanzu ana amfani da kalmar "Shah" a matsayin sunan uba ga yawancin mutane a Indiya, Pakistan da Afghanistan waɗanda suke Hindu, Musulmai da Jain. Sunaye da yawa na Indiya waɗanda ke da Shah a cikinsu; sanannen cikinsu shi ne Shah Jahan, wanda a matsayinsa na Sarkin Indiya ya ba da umarnin ƙirƙirar Taj Mahal . Aya daga cikin mahimman kalmomin da ake amfani da su a cikin chess shine matanin shah na Persia, ma'ana "sarki ba zai iya tserewa ba" [1]
Kalmar "Shah" galibi tana nufin Mohammad Reza Pahlavi, Shah na Iran daga 1949 zuwa 1979.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Shah Of Persia
-
Mutum-Mutumin Sarkin/Shah na Medesi
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.