Sheikh Ahmad Abulfathi Alyarwawee

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sheikh Ahmad Abulfathi Alyarwawee

Sheikh Ahmad Abulfathi (RTA) Babban malami ne wanda ya koyar kuma yayi umurni da a koyar da addinin islama,ta hanyar sufaye. Shehi (Murshid) ne na darikar Tijjaniya wanda kuma ya rayu a ƙasashen; Nijeriya, Nijar, Cadi da kuma Senegal tsakanin shekarur alif 1919 da shekara ta 2003 miladiya. Shi mutumin Konduga ne a Jihar Borno, Nijeriya.

Tarihin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Maula Sheikh Abulfathi (al kunyarsa da Shehu Ibrahim RTA ya sa masa) dan Aliyu ne, bin Ahmad bin Aliyu bin Muhammad Mustapha bin Muhammad Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hissain bin Sulaiman bin Ishaq bin Ali Zainnul Abideen bin Ahmad bin Muhammad Nafsu-Zakiyya bin Abdullahi Kamill bin Hassanul Musanna bin Hassannul Sibdi bin Aliyu bin Abi-Dalib (RTA).

Littattafan da ya Wallafa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya wallafa litatafai ma su yawa, a cikin su akwai;

  1. Ifadatul Kiram Fi’tarih Maulid Khairul Anam
  2. Al’ajiwiba Ahmadiyya Limasa’il Duniya Wa Tariqa Ahmadiiyya Tijaniyya
  3. Al’ajiwiba Ahmadiyya Fi Mas’ala Ibrahamiyya
  4. Alqatamas Fi sharhi suratul Ikhlas
  5. Tuhfatul Adfal Fi Nahwu
  6. Takrib Qawa’id Irab Limubta’idina Minal Dulab
  7. Jawahir Rasa’il
  8. Hilasatu Jawhar Fi Qawa’id ilmi Ma’ani Wal Bayan
  9. Rihilatu Ahmad Yarwa Litalbiyati Da’awatu Turk Sufiyah Fi Biladi Maghribiyah
  10. Risalatu Faydha Rabaniya Fi Taqyid Shrud Tariqa Tijaniyya
  11. Risatu Fi Sujud Sahwu
  12. Rihilatu BaRriya Wa Bahriya Liziyarutu Sahibil Asar
  13. Ziyadatu jawahir
  14. Shaddu Rihal Fi Hajj Wa Umrah
  15. Sharhu Jawharatu Kamal
  16. Fathu Al’ali Kareem Fi Salati Ala Nabiyul Azeem
  17. Kanzul Rashad Fi Wa’azu Wal Irshad
  18. Mu’ayin Dalib Alragib Fi Ma’arifatu Mustala’a Hadith
  19. Nata’ij Asfar Fi Salati Ala Sayedina Muhammad Nabiyi Mukhtar
  20. 2Wamdatu Min Durar Sheikh Abulfathi

Wafati/Rasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Shehi yayi wafati a ranar Laraba 21 ga watan Safar 1424 A.H. wanda yayi daidai da 23 ga watan April 2003. Ya bar matan aure hudu da yaya arbain da uku.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]