Jump to content

Shirin "The Pearl of Africa"

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shirin "The Pearl of Africa"
Asali
Lokacin bugawa 2016
Asalin suna The Pearl of Africa
Asalin harshe Turanci
Ƙasar asali Sweden, Kenya, Thailand da Uganda
Characteristics
Genre (en) Fassara documentary film, adventure film (en) Fassara, drama film (en) Fassara da LGBT-related film (en) Fassara
During 92 Dakika
Direction and screenplay
Darekta Jonny von Wallström (en) Fassara
Samar
Editan fim Jonny von Wallström (en) Fassara
Other works
Mai rubuta kiɗa Jonny von Wallström (en) Fassara
Director of photography (en) Fassara Jonny von Wallström (en) Fassara
External links

The Pearl of Africa wani fim ne na labarin gaskiya wanda Johnny von Wallstroem ya bada umurni, da ke mayar da hankali kan rayuwar Cleopatra Kambugu, wata mata da aka haifa a Uganda wacce ta yanke shawarar bayyana jinsin ta na daudu[1] duk da rashin jituwa ga dangantakar jima'i a tsakanin jinsi guda a kasar.

Kalmar "Pearl of Africa" na da danganata ga Winston Churchill wanda ya yi amfani da kalmar wajen kwatanta sassan tsirrai na flora da fauna na Uganda.[2]

Bayani a taƙaice

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2014, lokacin da jarumar da masoyinta suka yanke shawarar zama cikin aminci, kasar Uganda ta zartar da dokar luwaɗi; daga baya a cikin shekarar, wani tabloid na Uganda, Red Pepper, ya fitar da Kambugu, wanda a ƙarshe ya tilasta wa masoyan tserewa daga Uganda. A Sweden, darekta Johnny von Wallstroem na shirya fim game da ɗan luwadi ɗan gudun hijirar Uganda. Duk da haka, jarumin fim ɗin ya yi sanyi lokacin da ya ji tsoron cewa za a iya cutar da iyalinsa a Uganda. Daga nan Wallstroem ya tafi Uganda don bincika labarai game da mutanen LGBT waɗanda suka himmatu don bayyana kansu a bainar jama'a. An gabatar da shi ga Kambugu, wanda da farko ya yi shakka amma ya yanke shawarar bayyana kanta da kuma jinsinta a gaban kyamara. Duk mutanen biyu sun fara haɗin gwiwa a kan jerin sassan yanar gizo mai sassa bakwai, The Pearl of Africa, wanda ya haifar da aiwatarwa da samar da shirin gaskia.[3]

Fim din ya ba da labarin Kambugu, wanda aka haifa namiji amma ya koma mace da tafi so a ko da yaushe duk da gaba da nuna kyamar hakan a kasarta. Har ila yau, ya shafi dangantakar da ke tsakanin Kambugu, wanda dan gwagwarmaya ne da kuma masoyinta Nelson, mutumin kirki da gwagwarmayar su da kuma ƙaunar juna.

Sakin shirin

[gyara sashe | gyara masomin]

An nuna fim ɗin a bikin HotDocs Festival a watan Yuli 2016,[4] da kuma yayin bikin Joburg Film Festival na watan Disamban 2016.[5]

  1. Blignaut, Charl (May 29, 2016). "Radicalacts of love". City Press.
  2. "Why Uganda is called the Pearl of Africa?". www.atta.travel. Retrieved 2021-01-30.
  3. "Wise, Damon (November 20, 2016). "'Pearl of Africa' Challenges Media Stereotypes of Trans People and Africa: 'It's Not Ebola All the Time'". Variety. Retrieved 26 March 2017.
  4. La Rose, Lauren (July 14, 2016). "Transgender Women Find A Voice; Heart-wrenching docs humanize and universalize their stories". Barrie Examiner.
  5. New Desai film locates the moment when things fell apart". Star, The. October 28, 2016.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]