Sinasir
Appearance
Sinasir wani abinci ne na Najeriya da ake yi da shinkafa wanda ya shahara a yankin arewa. [1] Nau’in shinkafar da ake amfani da ita iri biyu ce: Dafaffe da jikakken shinkafa. [2] [3] [4]
Ana shirya abincin da shinkafa ne ta hanyar haɗawa dafaffe da jikakken shinkafar da aka gauraye a soya. Sauran sinadaran da ake amfani da su sun haɗa da sukari, gishiri, madara, kwai, albasa, da man kayan lambu. [5]
Sinasir na ɗaya daga cikin girke-girke masu daɗi da yawa a arewacin Najeriya. Ana yin shi da ɗan gajeren shinkafa iri ɗaya da ake yin tuwon shinkafa. [1]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "How to Make Sinasir Recipe - Northpad Nigeria". northpad.ng (in Turanci). 2022-01-30. Retrieved 2023-02-14.
- ↑ omotolani (2018-02-20). "This rice pancake recipe is giving us food goals". Pulse Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2022-06-30. Retrieved 2022-06-30.
- ↑ Health, Public (2020-06-10). "5 Health Benefits of Masa (Waina /Sinasir) - Public Health" (in Turanci). Retrieved 2022-06-30.
- ↑ "Sinasir". ResearchGate.
- ↑ "Sinasir (Rice Pancakes)". Daily Trust (in Turanci). 2020-12-27. Retrieved 2022-06-30.