Suratul Maryam
![]() | |
---|---|
Surah | |
Bayanai | |
Suna saboda | Maryam a Musulunci |
Akwai nau'insa ko fassara | Maryam da Maryam |
Harshen aiki ko suna | Larabci |
Suratul Maryam (Larabci: مريم, Maryam ; Larabci ma'anar "Maryama") ita ce surah ta goma sha tara (19)(sūrah) Acikin Al-Qur'ani mai girma ayoyinta 98 (āyāt). Dukkanin surori 114 na cikin Al-Qur'ani an tsara sune daidai da tsarin da aka bi tun lokacin Khalifa Usman. An sanyawa ita wannan surah ta Al-Qur'ani mai girma suna Maryam ne saboda a cikinta an bada labarin Maryamu, mahaifiyar Annabi Isah (Yesu) alaihis salam. A cikinta an ba da labarin abubuwan da suka faru kafin haihuwar Yesu, batun da ke cikin Luka 1 na Baibul ɗin Kirista. Ayoyin cikin surar sun yi bada labaran sanannun annabawa da yawa, wanda suka haɗa da Ishaku, Yakubu, Musa, Haruna, Isma'il, Idris, Adam, da Nuhu.
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]