Tajudeen Abdul-Raheem

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tajudeen Abdul-Raheem
Rayuwa
Haihuwa 6 ga Janairu, 1961
ƙasa Najeriya
Mutuwa 25 Mayu 2009
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara (traffic collision (en) Fassara)
Karatu
Makaranta St Peter's College (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam da Malami
Kyaututtuka

Tajudeen Abdul-Raheem, (6 Janairu 1961 - 25 Mayu 2009), ya kasance babban sakatare na kungiyar <i>Pan-African Movement</i>, kuma ya kasance darektan J<i>ustice Africa</i>, sannan mataimakin darektan Majalisar Dinkin Duniya Campaign Millennium for Africa na wani shiri na Majalisar, kuma marubuci ne a jaridu daban-daban haka nan da mujallu a duk faɗin duniya akan Afirka.

An haifi Tajudeen a garin Funtua a Jihar Katsina da ke Najeriya a cikin watan Janairu shekarar 1961, kuma ya rasa ran shi a wani hatsarin mota a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2009 a birnin Nairobi na kasar Kenya, yayin da yake a hanyar zuwa filin jirgin sama domin hawa jirgi zuwa kasar Rwanda inda zai gana da shugaban kasar Paul Kagame. [1]

Ya sami digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa daga jami'ar Bayero, da ke Kano haka nan ya kasance malamin Rhodes a Oxford, ya kuma samu PhD daga jami'ar Buffalo .[2][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. http://news.bbc.co.uk/2/hi/africa/8067260.stm
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-08-27. Retrieved 2021-07-15.
  3. https://www.pambazuka.org/governance/tributes-fallen-giant

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]