Tara Fela-Durotoye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tara Fela-Durotoye
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 6 ga Maris, 1977 (47 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar Lagos
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mai kwalliya da ɗan kasuwa
Fela Durotoye

Tara Fela-Durotoye (haihuwa 6 ga Maris 1977)[1]yar'Najeriya ce, lauya kuma mai kasuwanci. Ta kasance shahararriya a Najeriya cikin masu yin sana'ar kwalliya, Ta samar da 1999, kuma ta kafa makarantar kwalliya a Nigeriya.

Itace ta kafa kuma take shugabancin House of Tara International[2] Kuma wacce ta kirkiri Tara Orekelewa Beauty range, Inspired Perfume da H.I.P Beauty range. Kuma ana mata kallon babbar yar'kasuwa cikin mata yan'kasauwa a Najeriya ganin cewa ta fara "Tara Beauty Entrepreneur" initiative. Ta kuma shiga koyarwa.

A 2007, Tara Fela-Durotoye an bata kyautar awarded the Africa SMME Award da kuma Entrepreneur award a South Africa[3] and in 2013, Forbes listed her as one 20 Young Power Women In Africa[4]

Kuma ita tsohuwar dalibar Lagos Business School Chief Executive Programme, INSEAD Abu Dhabi, Yale University, The Stanford SEED Transformation Programme, da kuma Harvard Kennedy School having completed the Global Leadership and Public Policy in the 21st century, har wayau ita mamba ce ta France/Nigeria Investment club wanda aka samar a 2018 ta hannun French President Emmanuel Macron.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Tara Fela-Durotoye an haife ta ne a St. Nicholas Hospital, Lagos ga mahaifin ta John Ejegi Sagay, wanda kwamishina ne a Federal Civil Service, Nigeria taré da mahaifiyarta Felicia Omaghomi. Amma auren iyayen ta ya rabu sanda take wata takwas kacal; Kuma da kasancewa daga gidan mai mata da yawa, haka yasa ta taso a hannun kishiyar mahaifiyarta, Modupe Agnes Sagay. Ta fara makarantar ta a Command Children School, Victoria Island sannan ta cigaba a Nigeria Navy Secondary School, Ojo, inda ta kasance a makarantar kwana. A aji 5, ta zama firifet na Sanitary da Welfare Prefect. Ta gama jami'a a Jami'ar Jihar Lagos, tare da digiri a Law daga bisani ta kafa Tara International.

Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Tara tayi aure da Fela Durotoye,[5] wani hamshakin dan'kasuawa kuma mai bada shawarwari, chief executive officer na[6] Visible Impact. Ya bayyana muradinsa na takarar shugaban kasa a February 22, 2018, a karkashin jam'iyyar siyasa ta party Alliance for new Nigeria.[7] Suna da yara uku tare, Mobolurin, Demilade & Morolaoluwa.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ibukun Awosika, The Girl Entrepreneur
  2. ":: House of Tara | About Tara ::". houseoftara.com. Archived from the original on 2018-02-15. Retrieved 2017-12-22.
  3. "Africagrowth Institute - It is our business to help your business". www.africagrowth.com. Retrieved 2017-12-22.
  4. "The 20 Young Power Women In Africa 2013". Forbes. Archived from the original on 2017-02-02. Retrieved 2015-02-04.
  5. Fela Durotoye Archived 14 Mayu 2010 at the Wayback Machine
  6. Official Website of Visible Impact Archived 2 Mayu 2010 at the Wayback Machine
  7. [1]