Tashar Bas ta Oshodi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Tashar Bas ta Oshodi
Wuri

Tashar Mota ta Oshodi tana a unguwar Oshodi da ke Jihar Legas a Najeriya. Tashar motar dai tana tsakanin babban titin Legas zuwa Apapa da titin Agege. Tashar bas ta Oshodi ta kasu kashi uku da ake kira: Terminal 1, Terminal 2, da Terminal 3.[1]

Gina[gyara sashe | gyara masomin]

Wani kamfanin gine-gine mai suna Planet Projects Limited ne suka gina tashar bas ta Oshodi. An kiyasta aikin gina tashar ya ci kimanin dala miliyan 70. An gina tashar ne don ɗaukar kimanin motocin bas ɗin jigilar jama'a 820.[2]

Tashoshi da wurare[gyara sashe | gyara masomin]

Tashar bas Lagos-Oshodi
Public transportation in Lagos
Bas ɗin BRT (a sama) da bas ɗin LBSL (ƙasa)

Tashar bas ta Oshodi ta kasu zuwa tashoshi uku da ake kira: Terminal 1, Terminal 2, da Terminal 3. Kowace rukuni ta ƙunshi murabba'in mita 30000 kuma ta haɗa da wurare da yawa waɗanda suka haɗa da: wuraren saukar da kaya, wuraren siyan tikiti, wurin tuƙi, wuraren ajiye motoci, dakunan wanka da sauran su.[3] Tashar bas ta Oshodi ta fara aiki ne a watan Mayun 2019 kamar yadda dan kwangilar da ke kula da aikin ya sanar.[4] Terminal 1 na zirga-zirgar tsakanin jihohi ne, kuma an tsara shi ne don wuraren da ya shafi kudu maso yamma, kudu maso gabas, FCT, da jihohin Arewa.[5] Terminal na biyu don hanyoyin tsaka-tsaki ne. Ikeja, Agege, Iyana Ipaja, egbeda, Abule Egba da dai sauransu. Terminal 3 yana daukan hanya kamar Mile 2/Festac, Airport road, Bariga/New Garage, Tincan, Orile, Apapa/Wharf, ejigbo, Ajegunle/Boundary, Ojodu/Berger, Gbagada/Anthony, Eko Ijumota, Iyana Isolo/Jakande Gate/ Itire, Ojota/Ketu/Mile 12, Adeniji, Eko Hotel.[6]

Kaddamarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Tashar tashar sufurin jama'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da tashar bas din ta Oshodi a ranar 24 ga Afrilu, 2019, tare da tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, Gwamna mai ci, Babajide Sanwoolu, Abiola Ajimobi, Ibikunle Amosun da sauransu.[7]

Abin lura[gyara sashe | gyara masomin]

Young chess players at Oshodi, homeless children
Yanayin Chess a Oshodi

Tare da titin jirgin kasa na Oshodi, matasa daga yankunan talakawa suna wasan dara. A watan Disambar 2021, Fawaz Adeoye mai shekaru 19 da haihuwa ya lashe gasar gundumar 'yan watanni bayan an fara gabatar da shi a wasan.[8][9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Unveiling multi-level Oshodi multi-terminals". The Nations Nigeria. ADE etcYINKA ADERIBIGBE. 11 August 2020.
  2. "Buhari inaugurates Oshodi transport interchange built to accommodate 820, mass transit buses". Vanguard Nigeria. 24 April 2019.
  3. "$70 million Oshodi interchange has been successful, say officials". The Guardian. Adaku Onyenucheya. 8 June 2020.
  4. "Oshodi transport interchange to start operation May 2 – Contractor". Vanguard Nigeria. 23 April 2019.
  5. "Oshodi interchange: Lagos flags off inter-state commercial operation". The Nations Nigeria. Adeyinka Aderibigbe. September 2020.
  6. "Oshodi transport interchange". The Sun News. 11 May 2019.
  7. "Buhari commissions projects in Lagos". Premium Times. Olamide Fadipe. 24 April 2019.
  8. "Meet Homeless 19-year-old Fawaz Adeoye Who Emerged Oshodi Chess in Slum Champion". YouTube.
  9. "He Transformed the Most Dangerous Place in Lagos, Nigeria". YouTube.

Samfuri:Lagos