Ibikunle Amosun

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibikunle Amosun
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 2019 -
Lanre Tejuosho
District: Ogun Central
Gwamnan jahar ogun

29 Mayu 2011 - 29 Mayu 2019
Gbenga Daniel - Dapo Abiodun
District: Ogun Central
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Femi Okurounmu - Iyabo Obasanjo-Bello
District: Ogun Central
Rayuwa
Cikakken suna Ibikunle Oyelaja Amosun
Haihuwa 25 ga Janairu, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Olufunso Amosun (en) Fassara
Karatu
Makaranta University of Westminster (en) Fassara
Moshood Abiola Polytechnic (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Ibikunle Amosun (an haife shi a 25 ga watan Janairu shekarar 1958) Ɗan kudancin Najeriya ne, kuma Ɗan siyasa Wanda ya zama zaɓaɓɓen sanata mai wakiltar mazaɓar sanatan Ogun ta Tsakiya na Jihar Ogun, Najeriya April 2003. A watan April shekarar 2007 yanemi takaran gwamnan Jihar amma bai samu nasara ba. Ya sake neman takara a shekarar 2011, inda yayi nasara a ƙarƙashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN). Ya sake neman takarar gwamna a karo na biyu a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shekara ta 2015 kuma ya samu nasarar sake zaɓen sa, ya kama aiki a watan Mayun 29, shekarar 2015.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Amosun a ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 1958 acikin gidan Musulmai. Yayi makarantar firamare a African Church Primary school dake Abeokuta daga (1965–1970), sannan yaje African Church Grammar school, Abeokuta Dan yin karatun sakandare daga shekarar (1971 – 1977). Bayan nan ne yatafi Ogun State Polytechnic, inda ya kammala da Higher National Diploma (HND) a shekarar 1983. Amosun yasamu zamu mamba na Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) a shekarar 1990. Ya kuma zama fellow a shekarar 1996. Ya kuma zama mamba na Chartered Institute of Taxation of Nigeria (1998).

Amosun yafara aikin sa a matsayin audit trainee da kamfanin Lanre Aremu & Co. (Chartered Accountants) 1984. Sannan ya koma XtraEdge Consulting amatsayin managing consultant. Daga shekarar 1990 yana daga cikin hadakar Ibikunle Amosun & Co. (Chartered Accountants) a garin Lagos. Amosun yasake zuwa Jami'ar Westminster dake London, United Kingdom, inda yasamu Master of Arts a fannin International Finance a shekarar 2000.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Afrilun 2003, an zabi Ibikunle Amosun amatsayin sanata mai wakiltar Yankin Ogun ta Tsakiya. Yayi rashin nasarar zama Gwamnan Jihar a April 2007, yayi takara karkashin jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP), inda Gbenga Daniel ya doke shi. Ya kalubalance sakamakon zaben, amma a watan Augustan 2009 sai Ogun State Election Petitions Tribunal suka kore karar.[1]

Amosun yasake zama dan'takara a jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) a zaben April 2011 a Jihar Ogun na gwamnoni. A wani rehoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar a 12 February 2011, ya bayyana mai taimaka masa na cewa; Amosun yakoma jamiyyar Congress for Progressive Change (CPC), sai dai daga baya jiga-jigan jamiyyar ACN sunki amincewa.[2] Amosun ya lashe zaben da aka gudanar a 26 April karkashin jamiyyar ACN, da kuri'u da suka kai 377,489. Abokin hamayyar sa Adetunji Olurin na jamiyyar People's Democratic Party (PDP) shi kuma yasamu 188,698 na yawan kuri'u sannan Gboyega Isiaka na jamiyyar PPN yazo na uku da kuri'u 137,051.

A 2015 Amosun yasake neman gwamnati akaro na biyu. Inda yazabi, Yetunde Onanuga, amatsayin Mataimakiyarsa, saboda tsohon Mataimakin sa ya canja shekara zuwa jamiyyar adawa. Amosun yazabi Onanuga wanda ke aiki a Lagos State Ministry of Environment akan wasu masu son zama su uku.[3].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Tribunal again upholds Gbenga Daniel's election". Business Day. 28 August 2009. Archived from the original on 2021-02-13. Retrieved 2009-12-07.
  2. Olayinka Olukoya (12 February 2011). "2011: Senator Ibikunle Amosun Dumps ACN, Joins CPC". Nigerian Tribune. Retrieved 2011-04-29.
  3. How Amosun’s running mate emerged, 19 December 2014, VanguardNGR, Retrieved 17 February 2016