Yetunde Onanuga
Appearance
Yetunde Onanuga | |||
---|---|---|---|
2015 - 2019 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ibadan, 11 Satumba 1960 (63 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Olabisi Onabanjo | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Yetunde Onanuga (an haife ta 11 Satumba 1960) ƴar siyasan Najeriya ce wanda ta kasance mataimakiyar gwamnan jihar Ogun .
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Onanuga a asibitin Adeoyo da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a Najeriya. Mahaifinta shine FT Fabamwo.[1]
Ta yi karatu a jihar Ogun sannan kuma a Legas inda ta samu shaidar malanta. Daga baya ta kammala MBA a Jami'ar Jihar Ogun .
Tana aiki a ma'aikatar kula da muhalli ta jihar Legas lokacin da aka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar Ibikunle Amosun a 2015. Amosun shi ne ɗan takarar da ke kan kujerar amma mataimakinsa na baya ya koma jam'iyyar adawa. Amosun ya zaɓi Onanuga daga cikin mutane uku masu yuwuwar tsayawa takara. [2]
An zaɓi Onanuga mataimakiyar gwamna. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Onanuga: Round peg in round hole, 7 January 2015, The Nation Online NG, Retrieved 17 February 2016
- ↑ How Amosun’s running mate emerged, 19 December 2014, VanguardNGR, Retrieved 17 February 2016
- ↑ HID Awolowo passes on at 99 Archived 2015-10-16 at the Wayback Machine, 2015, ThisDayLive, Retrieved 18 February 2016