Jump to content

Tattaunawa:Gasar Rubuta Mukalan Mutane a Katsina

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Wannan shafin track ne na project da muka gama kwanannan, kuma dama munyi alkwari cewa zamu zayyano jerin mukalai da muka samar a yayin wannan gangami. idan ka duba wannan shafin [1] zaka ga inda mukayi alkwarin zayyano jerin mukalai da muka samar. Ina fata za'a bar shafin zuwa lokacin da za'a gama duba sakamakon project, watakila a iya gogewa a wannan lokacin.Uncle Bash007 (talk) 10:03, 5 ga Yuli, 2022 (UTC)[Mai da]

Barka dae Malam @Uncle Bash007, ba wai an goge shafin bane ga baki ɗaya ba, a'a an mayar da shine a "project namespace" wanda ake cema "Wikipedia" (wato zaka ga ya fara da "Wikipedia:", sai sunan shafin). Bamu da cikakken bayanin namespaces a Hausa, amma na tabbata zaka iya karanta na turanci (en:Wikipedia:Namespace) ka fahimta.
A taƙaice, duk ayyukan da suka shafi Wikipedia (irin event offline, da gasa da campaigns) zasu iya documenting abun amma a project namespace kaɗai wato dole ya fara da "Wikipedia:". Main namespace (wato inda sunan ne kawai, kamar Kano) ba'a rubuta komi sai articles na WIkipedia.
Misali zaka ga wannan shafin Wikipedia:Gasar Hausa Wikipedia ta Shekara-shekara inda akayi shi (akwai "Wikipedia:" a farko), in ka lura za ka ga ba'ayi shi a Gasar Hausa Wikipedia ta Shekara-shekara ba.
Shafinka yana nan a project namespace Wikipedia:Gasar Rubuta Mukalan Mutane a Katsina, in ka tashi haɗa report haka zaka bada link ɗin a yadda yake.
Ina fatan ka fahimce ni. Nagode. –Ammarpad (talk) 18:19, 5 ga Yuli, 2022 (UTC)[Mai da]
Ok Ammarpad nagane kuma na gamsu.. Nagode kwaraiUncle Bash007 (talk) 22:35, 5 ga Yuli, 2022 (UTC)[Mai da]