Jump to content

Tattaunawar user:Ab-DanKoɗo

Page contents not supported in other languages.
Sabon sashe
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa!

[gyara masomin]
Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, El-Abdallaah! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma ina fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a shafina na tattaunawa. Na gode.–Ammarpad (talk) 10:22, 1 ga Yuli, 2023 (UTC)Reply

Canza shekaru daga Numbobi zuwa kalmomi

[gyara masomin]

Aslm @El-Abdallaah, barka da zuwa Wikipedia ta Hausa.

Na lura ka fara yin wani salon "gyara" na canza shekarun haihuwa daga numbobi zuwa kalmomi, kamar wannan da wannan da ma wasu da yawa. Please ka daina. Babu buƙatar irin wannan gyara. Shekarun haihuwa a ingantacciyar Hausa ana rubuta sune da numbobi kuma babu ɓukatar kalmomi bayan haka.

Kalmomin ana furta sune a Hausar lafazi, lokacin da ake magana. Sannan kowane bahaushe ko mai koyon Hausa da yaga numbobin yasan abunda suke nufi, kuma zai karanta sune da kalmomi a zuciya lokacin karatu.

Domin ƙara fahimtar gyara da inganta muƙaloli a Wikipedia ta Hausa, da ma sauran shawarwari ka karanta wannan saƙon marabar.

Da fatan zaka gyara. –Ammarpad (talk) 10:35, 1 ga Yuli, 2023 (UTC)Reply

Za ka iya samun damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen U4C

[gyara masomin]

Ina tuntubar ku ne saboda kun riga kun kaɗa ƙuri'a a zaɓen da suka shafi Kwamitin Kula da Ɗabi'a na Duniya (U4C). Kuna iya cancantar kaɗa ƙuri'a a zaɓen U4C na yanzu, wanda aka buɗe yanzu kuma zai ƙare a ranar 2 ga Yuni 2026. Kuna iya samun ƙarin bayani game da 'yan takara da zaɓen a shafin zaɓe akan Meta, kuma daga nan za ku iya samun damar jefa ƙuri'ar da kanta. Shiga cikin waɗannan zaɓen yana da mahimmanci ga shugabancin al'ummomin Wikimedia, kuma lokacin da kuka ɓata kuna koyo game da 'yan takara da kuma kaɗa ƙuri'a ana yaba muku.

-- Tare da haɗin gwiwar U4C, Keegan (WMF) (talk)

Keegan (WMF) (talk) 17:20, 20 Mayu 2026 (UTC)Reply

(This message was sent to Tattaunawar user:Abdallaahpage2 and is being posted here due to a redirect.)