Jump to content

Thatayaone Mothuba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Thatayaone Mothuba
Rayuwa
Haihuwa Gaborone, 5 Mayu 1978 (46 shekaru)
ƙasa Botswana
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Notwane F.C. (en) Fassara2000-2003
  Botswana men's national football team (en) Fassara2001-200220
Nico United (en) Fassara2003-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Thatayaone Mothuba (an haife shi a ranar 5 ga watan Mayun 1978) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Botswana, wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nico United tun 2003.[1] An fara kiran Mothuba zuwa tawagar kwallon kafa ta Botswana a shekarar 2001, kuma yayi nasarar ciwa kasarsa wasanni biyu a shekarar 2002.[ana buƙatar hujja]

An haifi Thatayone Mothuba a ranar 5 ga watan Mayun 1978. Ya buga wa Botswana wasa a kasa da shekara 17,20,23, babbar tawagar kasar kuma yana cikin tawagar da ta lashe gasar Botswana 4 a lokacin da ya zura kwallo a ragar Namibiya. Kwararren mai tsaron baya ne wanda yake da hikimar kwatar kwallo. Ya lashe gasar zakarun Afrika tare da tsohuwar kungiyar kwallon kafa ta Notwane.[2] Yana cikin tawagar da ta buga kunnen doki babu ci a gasar COSAFA castle Cup a filin wasa na kasar Gaborone. A halin yanzu shi mataimakin koci ne a kulob ɗin Nico United a Selebi Phikwe, ya yi aiki tare da irinsu tsohon dan wasan kasar Zimbabwe Madinda Ndlovu, Luke Masumera, Paul Gundani.[ana buƙatar hujja]

  1. Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill ; et al. " Thatayaone Mothuba Olympic Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 13 August 2017.
  2. Thatayaone Mothuba at National-Football-Teams.com