Theo Walcott
Theo Walcott | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Theo James Walcott | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Stanmore (en) , 16 ga Maris, 1989 (35 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta |
Richard Taunton Sixth Form College (en) The Downs School (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da marubuci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | wing half (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 70 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 176 cm |
Theo Walcott (An haifeshi ranar 16 ga watan Maris, 1989). Tsohon dan wasan ƙwallon ƙafa ne dan asalin kasar Ingila. A shekarar alif dubu biyu da shida 2006 ya wakilci kasar Ingila a fasr cin kofin duniya. Haka zalika ya wakilci kasar tashi a gasar Euro wanda aka buga a shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2016 inda dan wasan ya buga wasanni guda arba'in da bakwai 47 inda ya samu nasarar jefa kwallaye guda takwas 8 a raga.[1]
Walcott kaya ne na kungiyar kwallon kafa ta Southampton academy, sannan kuma ya jona kungiyar kwallon kafar Southamptom kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal akan jumillar kudi £5m ashekara ta alif dubu biyu da shida 2006.[2] Saboda gudunsa da kuma iya tafiya da kwallo da kuma takonsa, mai bashi horo kuma babban koci wato Arsene Wenger ya maidashi dan wasan gefe a yawancin rayuwar kwallon shi. Dan wasan ya buga wasa a matsayin dan wasan gaba na tsakiya tun shekara ta alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa da goma sha hudu 2014 inda da yake yana cikin wadanda suka fi kowa zura kwallo a cikin raga inda ya samu nasarar jefa kwallaye sama da dari 100 a raga a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din.[3]
A ranar talatin 30 ga watan Mayu shekarar alif dubu biyu da shida 2006. Walcott ya zama dan wasa mai karancin shekaru a ƙasar Ingila inda yake da shekaru goma sha bakwai 17 da kuma kwanaki guda saba'in da biyar. A watan Disamba, dan wasan ya samu nasarar lashe gwarzon dan wasa mafi karancin shekaru inda yaci kyautar BBC young sport personally of the year. A ranarvshida 6 ga watan September shekarar alif dubu biyu da takwas 2008 ya fara buga gasar shi ta farko a matsayin kwararren dan wasa a gasar tsallakewa cin kofin duniya a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta kasar Andorra. Wasa na gaba kuma suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Croatia a ranar goma 10 ga watan September. Dan wasan ya kasance dan wasa mai karancin shekaru a tarihin kasar Ingila da ya zura kwallaye guda ukku ringis a wasa daya.[4]
Rayuwar baya
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi dan wasan inda baban sa ya kasance bakine dan kasar jamaica. Mamar dan wasan kuma ta kasance fara ce kuma baturiya yar kasar Ingila.[5] An haifeshi a yankin Stanmore dake Landan amma ya girma ne a Compton Berkshire yaje cocin Compton a makarantar firamare dake ƙasar Ingila da kuma makarantar downs. Ya tashi ne a matsayin mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool saboda babanshi yana daya daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta Liverpool.[6] Lokacin da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea suka tambaye shi ya zama yaron dauko kwallo, anan ya samu damar haduwa da yan kwallon da yake muradin haduwa dasu yan Liverpool.[7]
Aikin Kungiya
[gyara sashe | gyara masomin]Southamptom
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin kakar 2004–05, Walcott ya yi tauraro a cikin ƙungiyar matasa ta Southampton waɗanda suka kai wasan karshe na gasar cin kofin matasa na FA da Ipswich Town. Bugu da kari ya zama mafi karancin shekaru da ya taka leda a kungiyar ta Southampton, yana da shekaru 15 da kwanaki 175, lokacin da ya fito daga benci da Watford a watan Satumbar 2004. Duk da haka, bai buga gasar Premier ba, kuma Southampton ta koma gasar Championship a karshen kakar wasa ta 2004–05.[8]
Walcott ya buga wasansa na farko a waje da Leeds United a ranar 18 ga Oktoba 2005, kuma ya zama matashin matashin wanda ya zura kwallo a raga a Southampton bayan mintuna 25 na rashin nasara da ci 2-1. Ya sake zira kwallo a waje a Millwall kwanaki hudu bayan haka, kuma duk da haka a cikakken wasansa na farko a gida da Stoke City a ranar Asabar mai zuwa. Girman shahararsa kuma ya sa aka ba shi suna cikin manyan 'yan wasa uku na farko don kyautar gwarzon ɗan wasan matasa na BBC a ranar 11 ga Disamba 2005.[9]
Arsenal
[gyara sashe | gyara masomin]Walcott ya koma Arsenal a ranar 20 ga Janairu, 2006, kan kudi fam miliyan 5, ya kai fam miliyan 12 dangane da buga wasanni da kulob din. Kuɗin asali, wanda za'a iya biya ta kashi-kashi da aka ruwaito a cikin The Times yayin da £5 miliyan ya ragu, ƙarin biyar na £ 1 miliyan da za a biya bayan kowane sashe na gasar Premier goma, da kuma fam miliyan 2 a cikin "bayan kuɗi", an sake dubawa. zuwa fam miliyan 9.1 a cikin yarjejeniyar sulhu da aka amince a watan Maris 2008.[10] Walcott ya fara shiga ne a matsayin malami, bayan ya amince ya rattaba hannu kan kwantiragin ƙwararru a ranar haihuwarsa ta 17 a ranar 16 ga Maris 2006. A cikin Satumba 2008, kocin Arsène Wenger ya tabbatar da cewa Tottenham Hotspur, Chelsea da Liverpool duk sun yi sha'awar siyan shi.[11]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Theo Walcott". The Football Association. Retrieved 1 February 2013.
- ↑ Theo Walcott". Arsenal F.C. Retrieved 22 June 2017. If necessary, select season required from below "My year" subheading
- ↑ Walcott wins Young Sports award". CBBC Newsround. 10 December 2006. Retrieved 15 June 2016.
- ↑ Wilson, Steve (1 October 2008). "The kids are alright: Football's youngest ever". The Daily Telegraph. London. Archived from the original on 4 October 2008. Retrieved 16 June 2012.
- ↑ Don Walcott, father of Theo, is the British-born son of Jamaican parents". Daily Express. London. 4 October 2008. Retrieved 15 May 2010.
- ↑ Hugman, Barry J., ed. (2010). The PFA Footballers' Who's Who 2010–11. Edinburgh: Mainstream Publishing. p. 426. ISBN 978-1-84596-601-0.
- ↑ Theo Walcott: Why I'm a Liverpool fan". Liverpool F.C. 20 June 2006. Archived from the original on 25 February 2014. Retrieved 22 February 2014.
- ↑ Wilson, Jeremy (10 January 2006). "Walcott spoilt for choice as Saints do their sums". The Guardian. London. Retrieved 7 July 2006.
- ↑ Three stars up for BBC award". BBC Sport. December 2005. Retrieved
- ↑ Wilson, Jeremy (1 April 2008). "Southampton lose £2.9m over Theo Walcott". The Daily Telegraph. London. Archived from the original on 11 January 2022. Retrieved 22 February 2014.
- ↑ Taylor, Declan (12 September 2008). "Wenger – The day I knew I wanted Walcott". Archived from the original on 23 October 2013. Retrieved 28 April 2017.