Titilayo Laoye-Tomori

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Titilayo Laoye-Tomori
Rayuwa
Haihuwa 22 Disamba 1948 (75 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Otunba Grace Titilayo Laoye-Tomori (an haifeta a watan December 21, shekara ta alif 1948),[1] tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Osun ce,[2] Nijeriya kuma ta rike matsayin Kwamishinan Ilimi.[3] Ana mata inkiya da “Ipinle Omoluabi” a yaren Yarbanci.

Farkon Rayuwa da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Titilayo Laoye-Tomoru (an haife ta a ranar 22 ga watan Disamba, shekarar 1948) an haife ta a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ga iyalin Amon Oyeyemi Laoye. Ta fara karatun ta ne a makarantar St. Catherine Girls Grammar School Owe, sannan kuma Kwalejin Victory College, Ikare, kafin daga bisani ta cigaba daga Jami'ar Legas kuma ta kammala karatun digiri na farko a fannin tarihi a shekarar 1973. Ta sama shaidar difloma a fannin ilimi na (PGDE) a shekara ta 1978 sannan kuma ta samu digiri na biyu "Masters" a Public Administration a shekara ta 1984.[4]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ta kammala karatun ta a Jami'a, sai ta tafi Bautar Kasa na NYSC na shekara guda. Bayan ta gama bautar kasan na NYSC, an dauke ta a matsayin jami’ar ilimi a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a shekarar alif 1974. Ta yi aiki a can har tsawon shekaru shida kafin ta samu matsayin mataimakiyar magatakarda (registra) a Jami'ar Legas. Ita ce Babbar Mataimakin Magatakarda a lokacin da ta bar Jami'ar a shekarar alif 1989. A lokacin da take jami'ar ta rike matsayin "faculty officer", "establishment officer" da "admissions officer".

Daga bisani ta cigaba da aiki da kamfanin Coopers & Lybrand International, PFM Consulting Limited, and Industrial and General Insurance Plc. Har wayau, ta kafa kamfanin ta na ba da shawarwari wato Quints Management Consultants. An nada ta a Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya da ke Iyakantacce, Kungiyar Kula da Kiwon Lafiya (HMO) a matsayin babban darakta, mai kula da kudi da kuma Gudanarwa.[5]

Dangane da alakar ta da jam'iyyar Action Congress of Nigeria, ta fito takarar matsayin mataimakiyar Gwamna Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola a zaben shekara ta 2007. Hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke a ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba, shekara ta 2010 ya sanya su a ofis bayan shari’ar da aka kwashe shekara uku ana yi.[6]

Rayuwar mutum[gyara sashe | gyara masomin]

Tana da aure kuma yara huɗu da jikoki tara. A shekarar 2019, a lokacin da take shekaru 70, ta auri mai kamfanin MiCom, Prince Michael Ponnle, wanda ke da shekaru 80 a lokacin.[7][8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Anonymous (22 December 2018). "'Ex-Osun deputy governor, amazon of no equal'". The Nation. Retrieved 21 November 2020.
  2. Omofoye, Tunji (26 May 2017). "LAUTECH students protest closure of school". Guardian. Retrieved 21 November 2020.
  3. Metro (5 October 2019). "Photos: Ex-Osun deputy governor Titi Laoye Tomori remarries Prince Ponnle". PM News. Retrieved 21 November 2020.
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-29. Retrieved 2020-11-22.
  5. "Akintola, Lukmon (11 August 2018). "Titi Laoye-Tomori". Independent Nigeria. Retrieved 21 November 2020.
  6. Anonymous (5 October 2019). "Ex-Osun Deputy Governor Titi Laoye Tomori, 70, Remarries MicCom Boss, Prince Ponnle, 80". The Elites Nigeria. Retrieved 21 November 2020.
  7. Owolawi, Taiwo (6 October 2019). "Osun ex-deputy governor Titi Laoye-Tomori remarries at age 70 (photos)". Legit. Retrieved 21 November 2020.
  8. City People (7 October 2019). "EX-OSUN DEPUTY GOV. OTUNBA TITI LAOYE-TOMORI REMARRIES". City People Online. Retrieved 21 November 2020.