Jump to content

Tsaone Sebele

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tsaone Sebele
Rayuwa
Haihuwa 27 Oktoba 1993 (31 shekaru)
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Tswana
Sana'a
Sana'a dan tsere mai dogon zango
Athletics
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Tsaone Bakani Sebele (an haife ta ranar 27 ga watan Oktoba 1993) 'yar wasan tseren Botswana ce wacce ta ƙware a cikin tseren mita 100 da 200.

A tseren mita 100 ta kare a matsayi na takwas a gasar Afirka ta shekarar 2015 [1] kuma ta bakwai a gasar cin kofin Afirka ta 2018. Ta kai zagaye na 2 a 2017 Summer Universiade. A shekarar 2019, ta wakilci Botswana a gasar wasannin Afirka na 2019 da aka gudanar a Rabat, Morocco. [2] Ta fafata ne a tseren mita 100 na mata. [2]

A tseren mita 200 ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar wasannin Afirka ta 2015. Ta kuma yi gasa tare da tawagar Botswanan a wasan relay a shekarar 2017 Universiade.

Mafi kyawun lokacinta shine ɗakika 11.61 a cikin tseren mita 100, wanda aka samu a cikin watan Maris 2017 a Pretoria; da ɗakika 23.79 a cikin tseren mita 200, wanda aka samu a watan Satumban 2015 a Brazzaville. [1]

  1. 1.0 1.1 Tsaone Sebele at World Athletics Edit this at Wikidata
  2. 2.0 2.1 "2019 African Games – Athletics – Results Book" (PDF). Archived from the original (PDF) on 1 September 2019. Retrieved 7 September 2019.