Jump to content

Tunkiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Tunkiya mai gemu
Jaririyar tunkiya

sa hoto

Tunkiya wata dabba ce da take rayuwa a kasashen Afirka wanda yawancin dangin ta farare ne, musamman a kasar Hausa. Akwai ire-iren tunkiyoyi da dake a kasashen duniya, kuma ko wace kasa za ka samu da irin kalar tunkiyarta, misali kamar kasar Indiya irin kalar tunkiyarsu daban da ta kasar Angola. Kana kuma idan ka duba na kasar Najeriya su ma daban suke da na sauran kasashen.

Amfanin Tunkiya

[gyara sashe | gyara masomin]

A nahiyar Afirka musamman ma a Najeriya ana amfani da Tunkiya a lokutan bukukuwa wata ana yankawa don cin naman, kamar Sallar Idi karama da Sallar Idi Babba ko kuma ranar suna idan an yi haihuwa.