Umaru Argungu
Appearance
Umaru Argungu | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Shekarun haihuwa | 5 ga Janairu, 1959 |
Wurin haihuwa | Kebbi |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ɗan bangaren siyasa | Peoples Democratic Party |
Umaru Tafidan Argungu (an haife shi a ranar 1 ga watan Mayushekarar n 1959) an zaɓe shi Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa a jihar Kebbi. Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]
Argungu ya samu digirin digirgir (M.Sc) a fannin harkokin sufuri. Kafin zaɓensa a Majalisar Dattawa, ya kasance Babban Manaja, Ayyuka na Musamman, Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya da Shugaban Kamfanin. Bayan zaɓe, an naɗa shi a kwamitocin wasanni, asusun jama'a, sa hannun jari, sufurin ruwa, muhalli, sadarwa da sojojin sama.[1]