Ummul Darda as-Sughra

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Umm al Darda a matsayin Sughra al Dimashqiyyah ko Umm al Darda ƙarami, ƴar fikihu ce a ƙarni na 7 kuma ƙwararriyar Islama a Damascus da Urushalima . Ba za taba rudewa da Ummul Darda matar sahabi Abu Darda .

Tarihin Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Rayuwarta ta farko[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance marainiya ce a karkashin kulawar Abul Darda. Tun tana karama takan zauna da malamai maza a masallaci suna yin sallah a sahu-sahu tare da koyin karatun alqur'ani . Ta ce "Na yi ƙoƙari na bauta wa Allah ta kowace hanya, amma ban taɓa samun wanda yafi zama mafi kyau acikin Zama fiye da zamanta tare da wasu malamai ba."

Koyarwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Banda karatun ta a masallatan Damascus da Kudus tana koyarwa a gidanta. Yayin da wata malamar Ummul Darda ta shiga sashin maza na masallaci (a kowane hali haramun ne ga mata). Ta ji daɗin samun dalibai mata da maza. Hatta halifa 'Abd al-Malik bn Marwan dole ne a lura da shi a matsayin daya daga cikin ajujuwa da yawa.

KasancewartaUmm al-Darda ta himmatu wajen koyarwa, tana koyar da ɗalibai dayawa. Wata rana wata daliba ta tambaye ta game da samun dalibai da yawa: Mun gajiyar da ku? A haka ta amsa da cewa Kai (pl) ka gaji da ni? Na nemi ibada a cikin komai. Ban sami wani abu da yafi kwantar min da hankali ba kamar zama da malamai da musanyar ilimi da su. [1] Umm al-Darda ta nuna taqawa, kunya da rashin fasikanci a rayuwarta ta yau da kullum da karantarwa ta batare da an biyata kuɗi ba don isar da ilimi da rayuwa a kan kyauta da sadaka.

Ra'ayinta[gyara sashe | gyara masomin]

Ta bada fatawa, wadda har yau ake amfani da ita, ta bawa mata damar yin sallah a zaune ( tashahhud ) da maza. [2]

Ahmad bn Hanbal ya ruwaito daga Zaidu bn Aslam ya ce:

Abdulmalik ya kasance yana aika goron gayyata izuwawa ga Ummu Darda, sai ta ciyar a matsayin baqonta, sai ya yi mata tambayoyi game da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai ya ce: “Ya tashi wata rana ya kira kuyangarsa, sai ta zo a hankali, sai ya zage ta, sai ta c “Kada ka zagi, domin hakika Abud-darda ya ba ni labari cewa ya ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. ka ce “Wadanda suka zekai ba za su kasance masu shaida ba, kuma ba za su zama masu ceto ba a Ranar Kiyama .” [3] .

Ibrahim bn Abi Ablah yana kallonta a matsayin mace saliha kuma mai kunya. A cikin littafin Ibn Asakir ta’rikh madinat Dimashq, an rubuta Tarjamar al-nisa cewa: “ Na ga Umm al-Darda a Urushalima tana zaune a cikin mata matalauta. Wani mutum yazo ya raba musu kudi. Ya baiwa Ummul Darda fals (tagulla). Ta ce wa mabaratan: Asayi naman rakumi da shi. Shin wannan kudin ba sadaqah bane? Ummul Darda ta ce: ya zo mana ba tare da tambaya ba [4]

Gado[gyara sashe | gyara masomin]

Ummul Darda ta kasance a hannun Iyas bn Mu'awiya, wani muhimmin malamin hadisi a lokacin kuma alkali mai hazaka da cancantar da ba'a tantama akai, kasancewar tafi sauran malaman hadisai na lokacin, ciki har da fitattun malaman hadisi kamar su Hasanul. Basri dan Ibn Sirin . [5]

Kamar yadda akace abaya, kada a ruɗe sunan Ummu Darda a matsayin Sughra da Ummul Darda, matar sahabbai ko Sahabi. Sai dai Mohammad Akram Nadwi a cikin Al-Muhaddithat: Malaman Matan Musulunci a bangaren Fihirisa sun ninka nassosin Abu Darda da Umm al-Darda, don haka ya danganta ruwayar Ummu Darda da Sughra da Umm al-Darda. a matsayin matar Abu-darda. Don haka, ana iya cewa, akwai wata mata mai suna Umm al-Darda, wata fitacciyar malar hadisi kuma malamar Fiqhu a masallatan Dimashƙu da Urushalima, ta rayu a ƙarni na 7 kuma ta shiga halin girmamawa daga wajen halifa Abd. al-Malik bn Marwan.

An kafa cibiyar koyar da alkur'ani da hifz da tajwidi ga mata a kasar Bahrain da sunanta.

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Al-Mizzi, Tahdhib al-kamal, xxxv. 355
  2. Empty citation (help)
  3. Sahih Bukhari
  4. Ibn 'Asakir. Ta'rikh madinat Dimashq, Tarajim al-nisa, p. 430
  5. Empty citation (help)