Usman Albishir
![]() | |||||
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 District: Yobe North
1999 - 2003 District: Yobe North | |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | Nguru, 15 ga Yuni, 1945 | ||||
| ƙasa | Najeriya | ||||
| Mutuwa | 2 ga Yuli, 2012 | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
| Imani | |||||
| Jam'iyar siyasa |
All Nigeria Peoples Party All People's Party | ||||
Sanata Shehu Usman Albishir, (An haife shine a ranar 15 ga watan Yuni shekara ta alif 1945–ranar 2 ga watan Yuli shekarar ta alif 2012) ɗan Najeriya ne mai wakiltar mazaɓar Yobe ta Arewa a jihar Yobe. Mahaifinsa shine Alhaji Albishir Abdullahi.[1][2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Ya halarci makarantu kamar haka: Nguru Central Primary School a shekarar (1953–1954), Islamic Quaranic School shekarar (1954–1956), Hausari Primary School, Maiduguri shekarar (1956–1959), Nguru Senior Primary School, Nguru shekarar (1959 – 1960), Provincial Secondary. Makaranta, Maiduguri (Now Government College 1964 – 1968). Ya samu Takaddun shaida kamar haka: Takaddar Firamare ta Farko shekarar (1960), Jami'ar London Janar Certificate of Education (GCE 1966), Takaddar Makarantun Yammacin Afirka (1968). [3]
Kasuwanci
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan samun nasarar kammala karatunsa na farko, ya shiga harkokin kasuwancin gidansu, inda aka ba shi horo tare da koyar dashi sana'o'i da kasuwanci wanda ya kai ga ya iya ayyukan kasuwanci daban-daban da suka haɗa da masana'antu, jigilar kaya, jirgin sama, gine-gine da tallace-tallace.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]

Siyasarsa ta fara ne a shekara ta 1998, a lokacin riƙon ƙwarya na marigayi Janar Sani Abacha, inda ya tsaya takara kuma ya yi nasara da gagarumin rinjaye, inda ya zama ɗan majalisar dattawa a lokacin a ƙarƙashin jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP). A farkon jamhuriya ta huɗu a shekara ta 1999 ya tsaya takara kuma ya lashe zaɓen sanata a jam'iyyar All Peoples' Party (APP). A lokacin da yake majalisar dattawa, saboda sanin ƙwarewarsa ta mulki da gudanarwa, sai aka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattijai ta APP, muƙamin da ya riƙe daga watan Yuni 1999 zuwa Afrilu shekarar 2003.[4] Ya yi murabus ne bisa raɗin kansa. A cikin watan Yuni shekarar 1999, an naɗa Albishir a kwamitoci kamar haka, Banki da kuɗaɗe, Tsaro, Sufuri da Keɓancewa.[5]
Ya sake tsayawa takara kuma ya lashe zaɓen gundumar Yobe ta Arewa a watan Afrilun 2003, a jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP).[6]
Bayan sake zaɓe a shekarar 2003, an naɗa shi Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, amma ya yi murabus bisa matsin lamba a watan Disamba shekarar 2004.[7]
Albishir ya kasance ɗan takarar jam'iyyar ANPP a zaɓen gwamnan jihar Yobe a shekara ta 2007, inda gwamna mai ci Bukar Abba Ibrahim ya mara masa baya, kuma ya samu ƙuri'u 382 inda Sanata Mamman Bello Ali ya samu ƙuri'u 88 a zaɓen fidda gwani. Sai dai saboda al’amuran shari’a jam’iyyar ta tsayar da Bello Ali a matsayin ɗan takara kuma aka zaɓe shi. Albishir ya ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci, kuma karar ta ci gaba da zama a gaban kotuna har zuwa watan Fabrairun shekarar 2010, lokacin da Kotun Koli ta yi watsi da ƙaukaka ƙara na ƙarshe.[8] Daga baya Albishir ya koma jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da fatan lashe zaɓen gwamna na shekarar 2011 acikin wannan jam'iyya.[9]
A ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2011, a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP da aka gudanar a filin wasa na Damaturu, jihar Yobe, Usman Albishir ya doke tsohon ministan harkokin ƴan sanda Alhaji Adamu Maina Waziri da Malam Garba Umar inda suka samu tikitin takarar gwamna na jam'iyyar a zaɓen da akayi a watan Afrilun shekarar 2011. Injiniya Yakubu Bello ya janye daga takarar ne jim kaɗan kafin a fara zaɓen yayin da Hassan Saleh, tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, ya janye bayan ƴan kwanaki. Albishir ya samu ƙuri'u 388; Waziri ya samu 226 yayin da Garba Umar ya samu 46.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Usman Albishir ya rasu ne a sanadiyyar haɗarin mota a ranar 2 ga Yuli, 2012.[10][11]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://lite.judy.legal/amp/case/albishir-v-inec-4dd948f6-d431-42fd-a798-2c1faf48f931
- ↑ Damaturu, Hamza Idris (2010-04-09). "Yobe: As Albishir hops off ANPPAfter a long but fruitless legal battle Senator Usman Albishir is changing political platform. But to what end?". Daily Trust. Retrieved 2020-10-10.
- ↑ https://allafrica.com/stories/201207030400.html
- ↑ "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ "Congressional Committees". Nigeria Congress. Archived from the original on 2009-11-18. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ "Senators". Dawodu. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ Cletus Akwaya (December 5, 2004). "N100m Bribe Rocks ANPP Senate Caucus". Online Nigeria Daily News. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ "Yobe Guber: Albishir Loses At Supreme Court". Nigeria Newspapers Online. February 20, 2010. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ Joel Duku (April 5, 2010). "Clash of political gladiators in Yobe State". The Nation. Archived from the original on 2012-03-12. Retrieved 2010-06-23.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/5885-pdp-shocked-at-albishirs-death.html
- ↑ "PDP shocked at Albishir's death | Premium Times Nigeria". 2012-07-03. Retrieved 2020-09-27.
