Veronica Nnaji
Veronica Nnaji | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Umuaka (en) , 10 ga Janairu, 1940 (84 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Veronica Ogechi Nnaji (An haife ta a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 1940), ma'aikaciyar kiwon lafiya ce kuma ƴar siyasa a Najeriya. A shekarar 1979, ta kasance ɗaya daga cikin rukuni na farko na mata uku da suka fara zama a kujerar majalisar wakilai na ƙasar Najeriya.
Kuruciya da Ilimi.
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Nnaji a garin Umuaka a cikin watan Janairun shekarar 1940, ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴa bakwai na manomi Therea Ezendu da 'yar kasuwa Mathias Ezendu. [1] Ta yi karatu a makarantar Holy Rosary School a tsakanin 1948, zuwa 1955, [2] bayan haka ta sami horo a matsayin ma'aikaciyar jinya a Asibitin Our Lady of Lourdes da ke Ihiala daga shekarar 1956, zuwa 1960. [1] Sannan ta halarci Makarantar Tsabta wato School of Hygiene da ke Aba da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Nsukka, inda ta cancanci zama ma’aikaciyar kula da marasa lafiya a shekarar 1963. [1]
Aiki.
[gyara sashe | gyara masomin]Daga baya Nnaji ta yi aiki a Asibitin Amaigbo Joint Hospital da ke Nkwerre tsakanin shekarar 1963, zuwa 1965, bayan ta yi aiki a Gidan marayu da ke Okwelle har zuwa shekara ta 1970. [1] [2] Ta yi aure a shekara ta 1965, kuma ta haifi 'ya'ya biyar. [2] A 1974, ta mallaki asibitin. [2]
Siyasa.
[gyara sashe | gyara masomin]A zaɓen shekarar 1979, na ƴan majalisu, Nnaji ta kasance ƴar takarar jam'iyyar Nigerian People's Party a Isu kuma an zaɓe ta a matsayin 'yar majalisar wakilai. Tare da Abiola Babatope da Justina Eze, ta kasance ɗaya daga cikin mata uku na farko da aka fara zaɓa a majalisar dokoki (An zabi Esther Soyannwo a shekarar 1964, amma ba ta hau kujerar ta ba).[3] Ta yi aiki a majalisa har zuwa 1983.[2]