Vincent Leonard Price Jr. (Mayu 27, 1911 - Oktoba 25, 1993) ɗan wasan kwaikwayo ne na Amurka. An san shi da aikinsa a cikin fim din ban tsoro, galibi yana nuna masu laifi. Ya bayyana a kan shirye-shiryen dandali, talabijin, da rediyo, kuma a cikin fina-finai sama da 100. Price yana da taurari biyu a kan Tafiyar Daukaka ta Hollywood, ɗaya don fina-finai masu motsi sannan ɗaya don talabijin.[1]
Rawat da Price ya fara takawa ya kasance a matsayin jagora a cikin wasan kwaikwayo na 1938 mai suna Service de Luxe.
Price ya bayyana farfesa Ratigan a cikin fim din Disney mai suna The Great Mouse Detective (1986), kuma ya bayyana a cikin wasan kwaikwayo The Whales of August (1987),wanda ya ba shi lambar yabo ta Ruhu Mai Zaman Kanta don Dan Wasa Namiji na Musamma. Don aikin muryarsa a cikin Great American Speeches (1959),an zabi Price don Kyautar Grammy don Mafi Kyawun Magana.
Price ya kasance ma'aboci tara zane mai kuma ba da shawara kan zane-zane,t are da digiri a tarihin fasaha.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.