Wasan Shaɗi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wasan Shaɗi
Wasan Shadi

Wasan Shadi wasa ce da Fulani ke yin ta kuma tana ɗaya daga cikin bukukuwan Kasar Hausa. Babbar manufar wannan wasa ita ce nuna jarumta. A da kafin wannan ƙarnin Fulani sun ɗauka wannan al-adar da matuƙar muhimmanci musamman a lokacin bikin aure ko sallah.[1]

Yanda ake wasan[gyara sashe | gyara masomin]

Ana yin shaɗi ne a tsakanin manema aure, inda samarin zasu fito da bulali don gasar duka ta yadda duk wanda ya nuna gazawa to tabbas ya rasa wannan gasa kuma haka zalika ya rasa cancantarsa na zama ango a al'adance.[2] Matashi Bafulatani zai cire rigarsa, sai ya zauna ko a kan turmi, ko ya dogara kafa ɗaya a kan wani, da makamantansu.[3] Sai abokin shadinsa ya samo bulala(Ana wayan amfani da Bulalan icen tsamiya) ya rika zumbuɗa masa, shi kuma yana tsaye ko gezau ba zai yi ba. Idan ya jure wannan bulala zuwa adadin da ya dauka; wasu sukan dauki minti biyu har zuwa goma sha biyu, wasu ma har fiye, to sukan samu kwarjini a wajen maza sannan kuma su samu farin jini a wajen matafulani yan'uwansu.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

[5]

  1. "Al-adun gargajiya". rfi hausa.
  2. Masarautar Dutse (2015). Festivals and Ceremonies in Dutse Emirate. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.dutseemirate.com
  3. Barau A. S. (2007). The Great Attraction of Kano State. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.
  4. Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. [[University Press PLC]], Ibadan-Nigeria.
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-22. Retrieved 2022-10-22.