Yakubu Dogara
|
| |||||||||||
11 ga Yuni, 2019 -
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
6 ga Yuni, 2015 -
6 ga Yuni, 2011 -
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 | |||||||||||
| Rayuwa | |||||||||||
| Haihuwa | 26 Disamba 1967 (58 shekaru) | ||||||||||
| ƙasa | Najeriya | ||||||||||
| Karatu | |||||||||||
| Makaranta | Jami'ar, Jos | ||||||||||
| Sana'a | |||||||||||
| Sana'a | lauya da ɗan siyasa | ||||||||||
| Imani | |||||||||||
| Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||||||||||
| yakubudogara.com.ng | |||||||||||

Yakubu Dogara CFR[1] (an haife shi a ranar 26 ga watan Satumban shekara ta alif dari tara da sittin da bakwai 1967). Ya kasan ce ɗan Najeriya kuma ɗan siyasa.[2] Ya kasance lauya yayinda daga bisani ya zama sipika a majalisar tarayyan Najeriya na goma sha hudu (14) daga shekara ta 2015-2019.[3] Da farko Dogara ya kasance ɗan jam'iyyar PDP a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi. Daga bisani ya koma jamiyyar All Progressives Congress (APC).[4]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Dogara daga ahalin Yakubu Ganawuri da Saratu Yakubu dogara a shekara ta alif 1967,ranar 26 ga watan Disamba.
Ya fara makarantar Firamare aji 6 a Gwarangah primary School a shekara ta alif 1976. A wancan ƙaramar hukumar Tafawa Balewa na jihar Bauchi.[5]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Dogara Yayi Makarantar Firamare Gwarangah Primary School, Tafawa Balewa L.G.A a jihar Bauchi. A Shekarar 1975. Daga bisani yayi Bauchi Teachers College a Shekarar 1982. Inda ya tafi jamiar Jos, Plateau State, inda ya samu digirinsa na lauya. A shekara ta alif 1992. Daga shekara ta alif 1992 zuwa 1993 yayi makarantar samun shaidan zama lauya a jihar legas.
An kirashi zuwa Bar a shekara ta alif 1993. Inda daga baya yayi mastas dinsa a Robert Gordon University Aberdeen Scotland.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "FULL LIST: Okonjo-Iweala, Abba Kyari... FG nominates 437 persons for national honours". TheCable (in Turanci). 2022-10-02. Retrieved 2022-10-13.
- ↑ https://www.today.ng/topic/yakubu-dogara
- ↑ "Yakubu Dogara at 50". The Sun Nigeria. 2017-12-26. Retrieved 2022-03-02.
- ↑ "Dogara: I'm unaware my traditional title is suspended". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2022-01-26. Retrieved 2022-02-21.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2015-09-24. Retrieved 2021-05-09.