Yau Usman Idris
Yau Usman Idris | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kauru, |
Sana'a |
Yau Usman Idris kwararren masanin kimiyyar nukiliyar Najeriya ne kuma shine babban darekta na yanzu a Hukumar Kula da Nuclear ta Najeriya (NNRA).[1][2]Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi.[3][4][5]
Farkon rayuwa da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife Idris a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Ya samu Digirinsa na B.sc a Jami’ar Maiduguri a (1988), M.sc. Physics a Jami’ar Ibadan a (1992), da P.hD. Fannin kimiyyar nukiliya a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a (1998).[2]
Farkon tashe
[gyara sashe | gyara masomin]Idris ya yi aiki a wurare daban-daban a fannin makamashin nukiliya kuma yanzu shi ne darekta janar na Hukumar Kula da Nuclear ta Najeriya (NNRA). Gwamnatin jihar Kaduna ta nada shi kwamishinan muhalli da albarkatun kasa.[6]
Kwarewar Nuclear
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne mataimakin shugaban kungiyar kula da fasahar nukiliya ta Afirka (FNRA)
Babban mai kula da yankin Afirka na Hukumar Makamashi na Kasa da Kasa (IAEA)
Memba a kwamitin ba da shawara, Kungiyar Kasuwancin Nuclear Afirka.[2]
Rayuwar kashin kai
[gyara sashe | gyara masomin]Ya yi aure yana da yara.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://en.m.wikipedia.org/wiki/Yau_Usman_Idris#cite_note-4
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-25. Retrieved 2020-08-23.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-06-20. Retrieved 2020-08-23.
- ↑ https://newswirengr.com/2020/05/29/yau-usman-idris-appointed-as-dg-of-nigeria-nuclear-regulatory-authority/
- ↑ https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/05/28/buhari-appoints-idris-head-of-nigerias-nuclear-regulatory-body/
- ↑ https://en.m.wikipedia.org/wiki/Yau_Usman_Idris#cite_note-11