Jump to content

Yehoshua Hana Rawnitzki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yehoshua Hana Rawnitzki
Rayuwa
Haihuwa Odesa (en) Fassara, 13 Satumba 1859
Mutuwa Tel Abib, 4 Mayu 1944
Makwanci Trumpeldor cemetery (en) Fassara
Karatu
Harsuna Ibrananci
Yiddish (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da marubuci
Hoton yehoshua

Yehoshua Ḥana Rawnitzki ( Hebrew: יהושע חנא רבניצקי‎  ; ( an haifeshi a 13 ga watan Satumban 1859 kuma ya mutu aranar 4 ga watan Mayun 1944) mawallafin Ibrananci ne, edita, kuma mai haɗin gwiwa na Hayim Nahman Bialik .

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Yehoshua Hana Rawnitzki ga dangin Yahudawa matalauta a Odessa a shekara ta 1859. Ya fara aikin jarida a shekara ta 1879, ta hanyar ba da gudummawa da farko ga Ha-Kol, sannan ga wasu labaran lokaci-lokaci.[1] Shi ne edita kuma mawallafin Pardes, tarin wallafe-wallafen da aka fi sani da buga waƙar Hayim Nahman Bialik na farko, "El ha-Tzippor," a cikin shekarar 1892. Tare da Sholem Aleichem (ƙarƙashin pseudonym Eldad), Rawnitzki (ƙarƙashin pseudonym Medad) ya buga jerin feuilletons mai suna Kevurat Soferim ("Burial of Writers"). [1] Daga shekarar 1908 zuwa shekarar 1911, Rawnitzki da Bialik sun buga Sefer Ha-Aggadah ("Littafin Legends") tarin aggadah daga Mishnah, Talmuds biyu da wallafe-wallafen Midrash .

Rawnitzki ya koma Falasdinu a shekara ta 1921, inda ya shiga cikin kafa kamfanin buga littattafai na Dvir . Ya mutu a can a watan Mayu 1944.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]