Yushau Anka
Yushau Anka | |||||
---|---|---|---|---|---|
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 District: Zamfara West
1999 - 2003 District: Zamfara West | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Jihar Zamfara, ga Afirilu, 1950 (74 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Alhaji Yushau Mohammed Anka (Afrilu 1950 - 12 ga Oktoba 2020) an zabe shi Sanata mai wakiltar Mazabar Zamfara ta yamma a jihar Zamfara, Najeriya a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya. Wanda ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya rike muƙamin daga Mayu 1999 zuwa Mayu 2007.[1]
Tarihin Rayuwa.
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Anka a cikin Afrilun shekarar 1950, kuma ya sami digiri na M.Sc a fanin (Business Administration).
Siyasa.
[gyara sashe | gyara masomin]An zabe shi sakataren kudi na kasa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya.[2] Ya tsaya takarar gwamnan jihar Zamfara a jam’iyyar PDP a shekarar 1999, amma ya sha kaye a hannun Ahmed Sani Yerima na jam’iyyar All Nigeria People’s Party ANPP.[3]
Madafun iko
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan ya hau kan kujerar majalisar dattawa a watan Yunin shekarar 1999, an nada shi a kwamitocin da’a, harkokin kasashen waje, harkokin ‘yan sanda (mataimakin shugaban kasa), kasuwanci, harkokin cikin gida da harkokin gwamnati.[4]
A watan Agustan shekarar 2001, ya ce shirin Gwamnatin Tarayya na rage radadin talauci yana raba kudade ne kawai ga magoya bayan siyasa maimakon rage radadin talauci.[5] Anka ya canza sheka zuwa jam'iyyar ANPP a wa'adinsa na biyu na majalisar dattawa. A watan Mayun 2006, Anka ya yi magana game da shawarar sauya kundin tsarin mulki ta yadda shugaba Olusegun Obasanjo zai iya tsayawa takara karo na uku na shekaru hudu.[6]
Mutuwa.
[gyara sashe | gyara masomin]Ya rasu ranar 12 ga watan Oktoban shekarata 2020.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-19.
- ↑ "Yushau Anka". AfDevInfo. Retrieved 2010-06-19.
- ↑ Constance Ikokwu. "Battle for the North-west". ThisDay. Archived from the original on 2005-01-16. Retrieved 2010-06-19.
- ↑ "Congressional Committees". Nigeria Congress. Archived from the original on 2009-11-18. Retrieved 2010-06-19.
- ↑ Agaju Madugba (2001-08-16). "PAP is Ill-conceived, Says Senator". ThisDay. Retrieved 2010-06-19.[permanent dead link]
- ↑ Kola Ologbondiyan (May 5, 2006). "6 Senators Against, 5 for, 5 Evasive". ThisDay. Retrieved 2010-06-19.