Yves-Emmanuel Dogbé

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yves-Emmanuel Dogbé
Rayuwa
Haihuwa Lomé, 11 Mayu 1939
ƙasa Togo
Mutuwa 10th arrondissement of Paris (en) Fassara, 7 Nuwamba, 2004
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Marubuci, maiwaƙe, sociologist (en) Fassara da mai falsafa

Yves-Emmanuel Dogbé (10 Mayu 1939 - 7 Nuwamba 2004) marubuci ne ɗan ƙasar Togo, masani a fannin falsafa, kuma masani ne a fannin ilimin zamantakewa, kuma malami.

Rayuwa da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Dogbé a Sa-Kpové, kusa da Aneho. [1] Ya karanci ilimin zamantakewa a birnin Paris kuma ya sami digiri na uku a jami'ar Paris Descartes.[1]

A matsayin sa na marubucin wasu manyan ayyuka goma sha biyar, Dogbé yana da babban matsayi a cikin marubutan Togo masu magana da harshen Faransanci. Ya fara yin suna tare da Affres, littafin wakoki daga shekarun 1966. An rubuta Tatsuniya na Afirka a ƙarƙashin rinjayar Jean de La Fontaine. Ya rubuta litattafai guda biyu na zamantakewa, La Victime game da wariyar launin fata da Incarcéré game da ɗaurinsa. Dogbé ya rubuta kasidu da yawa, musamman La Crise de l'éducation (1975).[2]

An kama Dogbé a Lomé a cikin shekarar 1977 saboda sukar manufofin tattalin arziki na gwamnatin Gnassingbe Eyadéma. Ya koma birnin Paris, inda ya kafa kamfanin wallafe-wallafen sa a shekarar 1979 ya kuma sa masa suna "Akpagnon" sunan mahaifinsa. Ya wallafa Anthology of Togo Poetry and Tales and Legends of Togo (a harshen cikin Faransanci da Ewe) a cikin shekarar 1980. A cikin shekaru masu zuwa, kamfaninsa ya wallafa marubutan Togo da yawa kuma kusan kowane aikin Dogbé da kansa. Ya kasance a gudun hijira har zuwa shekara ta 1991, lokacin da ya koma Togo.[1]

Ya mutu a Paris.[3][1]

Karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

Dogbé ya sami kyautar rayuwa ta Grand Prix littéraire d'Afrique noire a cikin shekarar 2002. [4]

Kamus na Tarihi na Togo (1996) ya kira shi "Babban marubuci mai rai na Togo." (living writer)[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Abalo Essrom Kataroh, Yves-Emmanuel Dogbé : l'homme et l'œuvre, Ed. Akpagnon, Lomé, 1997, p. 157 (as seen in Koffi Anyinefa, Le Togo littéraire, December 2009 ) Cite error: Invalid <ref> tag; name "ABA" defined multiple times with different content
  2. Satchivi, Ekoué (27 November 2013). "Yves Emmanuel Dogbè: Un passionné des belles lettres". Auteurs Togolais.
  3. 3.0 3.1 Decalo, Samuel (1996). Historical Dictionary of Togo. Scarecrow Press. p. 114. ISBN 9780810830738.
  4. "Winners of the Grand prix littéraire d'Afrique noire" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2016-03-03. Retrieved 2023-12-29.