Jump to content

Zainab Abubakar Alman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zainab Abubakar Alman
Rayuwa
Haihuwa 14 ga Janairu, 1965 (59 shekaru)
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Sana'a



   


 

Zainab Abubakar Alman, tsohuwar ‘yar majalisar dokokin a jihar Gombe ce kuma babbar daraktar mata da ci gaban jama’a (ARC-P), a karkashin gwamnatin Muhammad Inuwa Yahaya .

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Alman a ranar 14 ga Janairu, 1965, a karamar hukumar Kaltungo, jihar Gombe . Ta halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, inda ta samu Difloma ta kasa (OND) kan ci gaban al'umma a shekarar 1991.

Alman ya yi aiki da Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar Gombe a matsayin Jami’in Raya Al’umma, Sufeto, da Shugaban Sashe tsakanin 1987 zuwa 2000.

A shekara ta 2000, ta zama zaɓaɓɓen kansila a karamar hukumar Kaltungo. A tsakanin shekarar 2000 zuwa 2007 aka zabe ta a matsayin ‘yar majalisar dokokin jihar Gombe inda ta zama mataimakiyar bulala kuma shugabar kwamitin kula da harkokin mata/matasa.

A cikin 2021, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya nada ta a matsayin Darakta Janar, Mata da Ci gaban Jama'a (ARC-P).

A watan Maris 2022, an zabe ta a matsayin shugabar mata na shiyyar Arewa maso Gabas a jam'iyyar All Progressive Congress (APC)