Babbar Hanyar Ruwa (China)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Babbar Hanyar Ruwa
Gcjiangnan1.JPG
General information
Tsawo 1,776 km
Yawan fili 20,819.11 ha
55,629 ha
Labarin ƙasa
Map
Geographic coordinate system (en) Fassara 30°15′41″N 120°13′26″E / 30.261388888889°N 120.22388888889°E / 30.261388888889; 120.22388888889
Kasa Sin
Mountaineering (en) Fassara
First ascent (en) Fassara 2016
Darussan Babban Canal

Babbar Hanyar Ruwa wanda akafi sani a Birni Sin da Jing – Hang Grand Canal yana daga cikin wuraren tarihi na UNESCO, kuma shine hanyar ruwa ko kuma kogi da ɗan adam ya kirkira wanda yafi kowanne tsawo a duniya. [1]

Yana farawa a Beijing ; ya ratsa ta Tianjin, Hebei, Shandong, Jiangsu da Zhejiang ; kuma ya ƙare a Hangzhou .

Ya haɗu da koguna biyu mafi tsawo na ƙasar Sin: Kogin Yellow River da kuma Kogin Yangzi.

An gina tsofaffin ɓangarorin magudanar ruwa a lokacin karni na 5 BC.

Daular Sui (581-618 AD) ta ƙara wasu sassa. Tsakanin 1271-1633, daular Yuan (ta hanyar Guo Shoujing da sauransu) da daular Ming sun inganta ta kuma sun gina sassa don kai ruwa zuwa Beijing.

Jimlar tsawon ta ya kai kimanin 1,776 kilometres (1,104 mi). Iyakar tsayinsa shine 42 m (138 ft) a kusa da tsaunukan Shandong. [2]

Daular Song (960-1279) injiniya Qiao Weiyue ya ƙirƙira kulle fam a ƙarni na 10. Wannan ya bawa jiragen ruwa damar yin tafiya sama da kasa ta hanyar magudanar ruwa. [3]

Hanyar ta ba mutane da yawa mamaki a cikin tarihi gami da kuma malamin Jafananci Ennin (794-864), masanin tarihin Farisa Rashid al-Din (1247-1318), jami'in Koriya Choe Bu (1454-1504), da kuma mishan na Italiya Matteo Ricci (1552-1610). [4] [5]

A tarihi, ambaliyar ruwan Kogin Yellow ya yi barazanar fasa hanyar. A lokacin yaƙi ma ana amfani da mashigar a matsayin makami: dikes na Kogin Yellow wani lokaci ana fasa su don ambaliyar sojojin abokan gaba. Amma wannan ya haifar da bala'i da cutar da tattalin arziki.

Hanyar Ruwan ya inganta tattalin arzikin kasar Sin matuka kuma ya kara jawo harkokin kasuwanci tsakanin arewa da kudancin kasar. Har yanzu ana amfani dashi sosai har zuwa yau.

Wurin Tarihi ne na UNESCO.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Hutchinson's Encyclopedia Archived 2012-03-23 at the Wayback Machine, Encarta[permanent dead link]. 2009-10-31.
  2. Needham, Volume 4, Part 3, 307.
  3. Needham, Volume 4, Part 3, 350–352
  4. Needham, Volume 4, Part 3, 308 & 313.
  5. Brook, 40–51.