Jump to content

Zanzan Atte-Oudeyi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zanzan Atte-Oudeyi
Rayuwa
Haihuwa Lomé, 2 Satumba 1980 (44 shekaru)
ƙasa Togo
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Togo1999-2006362
JS du Ténéré (en) Fassara2001-2001
Satellite FC Abidjan (en) Fassara2002-2002
Beerschot A.C. (en) Fassara2002-200370
K.S.C. Lokeren Oost-Vlaanderen (en) Fassara2003-2006321
Football Club Molenbeek Brussels Strombeek (en) Fassara2006-2008291
CS Otopeni (en) Fassara2008-200910
  CF Montreal2009-2009120
Montreal Impact (en) Fassara2009-2009150
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 176 cm

Mohammed Zanzan Atte-Oudeyi (wanda aka fi sani da Zanzan; an haife shi a ranar 2 ga watan Satumba, 1980 a Lomé ) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Togo mai ritaya.

Zanzan ya fara taka leda a JS du Ténéré a gasar Firimiya ta Nijar da kuma kungiyar Satellite FC a Cote d'Ivoire, kafin ya koma buga wasa a Belgium a shekara ta 2002.

Zanzan ya buga wasa na tsawon shekaru shida a rukunin farko na Belgium, da Germinal Beerschot, Lokeren da FC Brussels,[1] kuma ya taka leda a takaice a gasar Romanian I na Otopeni, kafin ya ci gaba da aikinsa a Arewacin Amurka.

A ranar 15 ga watan Afrilu, 2009, Zanzan ya sanya hannu a kulob ɗin Montreal Impact na Rukunin Farko na USL. [2] Ya buga wa tawagar Canada wasanni 12 kafin ya tafi a karshen Nuwamba 2009. A cikin shekarar 2012, ya sanya hannu kan kwangila a ƙungiyar FC Eksaarde A Belgium. Wanda shine kashi na uku.[3]

Ƙasashen Duniya

[gyara sashe | gyara masomin]

Zanzan ya kasance mai taka-leda a tawagar kasar Togo tun shekarar 1999, inda ya fara buga wasansa na farko tun yana dan shekara 19. Ya kasance cikin tawagar kasar Togo a gasar cin kofin kasashen Afrika a 2006.

  1. "Stats Centre: Atte-Oudeyi Mohama Zanzan" . Guardian.co.uk . Retrieved 2009-10-14.
  2. "Nouvelles" . Montreal Impact (in French). Retrieved 2018-05-22.
  3. "David Testo Back For Two Seasons" . OurSports Central . 2009-11-30. Retrieved 2018-05-22.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]