Jump to content

Abdou Sidikou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdou Sidikou
Minister of Foreign Affairs of Niger (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Kouré, 1927
ƙasa Nijar
Mutuwa 26 ga Yuli, 1973
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya
Abdou Sidikou, 1962

Abdou Sidikou (An haude shi a shekarar 1927, ya rasu a shekarar 1973) ɗan siyasan Nijar ne kuma jami'in diflomasiyya. Sidikou shi ne Ministan Harkokin Wajen Nijar daga shekarar 1967-1970 a ƙarƙashin Hamani Diori.[1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]
Abdou Sidikou

An haifi Abdou - sunan mahaifinsa a Kouré, Niger a 1927. A ƙarƙashin mulkin mallaka na Faransa ya kasance dan wani shugaban yankin da aka nada, ko Chef du Canton, ya yi karatu a fitaccen École normale supérieure William Ponty a Dakar sannan daga baya ya yi karatun Likita a Kwalejin Magunguna ta Paris, ya kammala karatunsa a shekarata 1956, kuma ya fara aiki a Asibiti na Seine [2] a Faris, sannan kuma ya zama babban Masanin harhaɗa magunguna a Asibitin Ƙasa (Niamey)

Ayyukan Gwamnati

[gyara sashe | gyara masomin]

A 1959, an nada Abdou a matsayin darektan majalisar minista na farko na Kiwon Lafiya na Diallo Boubakar, sannan a 1962 aka nada shi Jakadan Nijar a Amurka, Kanada, da Majalisar Ɗinkin Duniya. A 1964 ya koma Jamus, inda ya kasance Jakadan Nijar a Yammacin Jamus, Austria, da Benelux da Scandinavia, da ƙungiyar Tattalin Arzikin Turai . Ya zama Sakataren Ministan Harkokin Waje a Yamai, kuma a ranar 14 ga Afrilun shekarar 1967, ya karɓi aikin daga hannun Shugaba Hamani Diori . Saboda rashin lafiya, ya sa aka nada shi a matsayin "Sakataren Harkokin Waje na Shugaban Ƙasa" a watan Janairun 1970, a wancan lokacin yana matsayin mukamin minista. Ya mutu 26 Yuli 1973.

  1. He was a member of the ruling PPN-RDA party.Decalo, Samuel (1997). Historical Dictionary of the Niger (3rd ed.). Boston & Folkestone: Scarecrow Press. ISBN 0-8108-3136-8.:pp. 16–17
  2. "Hôpital privé de la Seine-Saint-Denis"