Abdullahi Bala Lau
| Rayuwa | |
|---|---|
| ƙasa | Najeriya |
| Karatu | |
| Harsuna | Hausa |
| Sana'a | |
| Sana'a | Malamin addini |
| Fafutuka | Salafiyya |
| Imani | |
| Addini | Musulunci |
Abdullahi Bala Lau, wanda aka fi sani da Sheikh Bala Lau, Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya Malami, mai tafsiri, kuma mai wa’azi. Shi ne Shugaban Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah wa Ikamatus Sunnah.[1][2] Babbar Ƙungiyar Salafiyya a Najeriya[3] tun Disamba, shekara ta 2011.[4][5]
Life
[gyara sashe | gyara masomin]Sheikh Bala Lau haifaffen jihar Taraba ne. A shekara ta 2020 daya daga cikin mujallar Najeriya ta bayyana cewa shugaban Izala ya mutu. [6][7]
An haifi Balalau kuma ya girma a Jihar Lau Taraba .
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Sheikh Abdullahi Bala Lau memba ne na kwamitin amintattu da kuma kwamitin aiki na tsakiya. Bala Lau shine Shugaban kungiyar Jama'atul Izalatul Bid'ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS) ta Kasa a Najeriya. Ya kuma zama Jami'in Hulɗa da Jama'a (PRO) na kungiyar, yana da shekara Sha tara (19), a jiharsa ta Taraba. An naɗa shi babban limamin masallacin Juma'a na Daubeli Juma'a na Yola ta arewa. Bayan wannan, ya zama memba na JIBWIS Kwamitin Zartarwa na ƙasa, ajin Wa’azi na ƙasa da kwamitin ƙaddamar da Shugaban. Sheykh Bala Lau ya zama Mataimakin Shugaban ƙungiyar na ƙasa bayan rasuwar Sheikh Abubakar Ikara. Sheikh Abdullahi shugaba ne abin koyi Wanda ya shahara wajen taimakon addini da neman hadin kan Musulman Najeriya da ma Afrika baki daya. Sheikh Bala Lau Malami ne kuma hamshakin dan kasuwa wanda wannan ne ya bashi damar taimakon marayu, gajiyayyu da sauran harkokin Addini.
Shugaban ƙungiyar Izala a Najeriya Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ƙaryata labarin mutuwarsa da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa a shafinta na intanet da kuma Twitter a ranar Lahadi.
Shiekh Bala Lau ya shaida wa BBC cewa "Ina nan lafiya lau." A labarin da ta rubuta da ya tayar da hankalin ƙungiyar Jama'atul Izalatul bid'ah wa Iqamatus Sunnah, Sahara Reporters ta ce shugaban ƙungiyar ya rasu a ranar Asabar. Ta kuma wallafa hotonan jana'iza a shafinta na Twitter tare da hoton gawar da ta ce ta Shiekh Bala Lau ce da aka yi jana'izarsa da safiyar Lahadi. A hirarsa da BBC, Shiekh Bala Lau ya ce "ba mu san dalilin rubuta wannan labarin ba. Ya kamata a tuntubi iyalinmu ko ƙungiyarmu ta Izala. "Rayuwa tana da farko kuma tana da karshe kamar yadda Allah ya karbi rayuwar Annabi SAW. Amma bai kamata ace jarida ta dauki labarin da ba ya da tushe ba. Wannan wata kiyayya ce." A nata bangaren ƙungiyar Izala bayan karyata labarin mutuwar shugabanta, ta bukaci Sahara Reporters ta fito ta gaggauta ƙaryata labarin da ta yaɗa. Shiekh Isa Ali Pantami, ya ce hotunan da Sahara Reporters ta wallafa na jana'izar Shiekh Adam Muhammad Gashua ne, tare da shawartar kafar ta fito ta gyara.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]__LEAD_SECTION__
[gyara sashe | gyara masomin]Abdullahi Bala Lau, wanda aka fi sani da Sheikh Balalau, masanin addinin Musulunci ne a Najeriya,kuma malamin addini, Muffassir, sannan mai wa'azi. Shi ne Shugaban kasa [8] na ,Jama'atu Izalatul Bidi'ah wa Ikamatus Sunnah, [9] babbar ƙungiyar Salafi a Najeriya, [10] tun watan Disamba na shekara ta 2011.
- ↑ "Nigeria: Sheikh Bala Lau Now Izala National Chair". allafrica.com. 16 December 2011. Retrieved 2020-12-24.
- ↑ "Sheikh Abdullahi Bala Lau – Sultan Foundation for Peace and Development". Archived from the original on 2021-05-12. Retrieved 2021-05-20.
- ↑ "Clottey interview with Sheikh Abdullahi Bala Lau, national chairman of Muslim Group JIBWIS | Voice of America - English". www.voanews.com.
- ↑ Day Izala regrouped in Kaduna[permanent dead link], Daily Trust, December 31, 2011.
- ↑ name="africascountry">Ochunu, Moses E. (25 January 2018). "Two Salafi Clerics Visit London". africasacountry.com. Retrieved 20 April 2020.
- ↑ "Is Renowned Islamic Scholar, Shaykh Bala Lau Dead?..." allnews.ng.
- ↑ Sharfadi, Basheer (May 10, 2020). "Sheikh Balalau yana nan a raye –Pantami".
- ↑ "Nigeria: Sheikh Bala Lau Now Izala National Chair". allafrica.com. 16 December 2011. Retrieved 2020-12-24.
- ↑ "Sheikh Abdullahi Bala Lau – Sultan Foundation for Peace and Development". Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved October 4, 2020.
- ↑ "Clottey interview with Sheikh Abdullahi Bala Lau, national chairman of Muslim Group JIBWIS". Voice of America. Archived from the original on May 20, 2021.