Abdullahi Yusuf Ahmed
Abdullahi Yusuf Ahmed | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
14 Oktoba 2004 - 29 Disamba 2008 ← Abdiqasim Salad Hassan (en) - Adan Mohamed Nuur Madobe (en) →
8 Mayu 2002 - 10 Oktoba 2004 ← Jama Ali Jama (en) - Mohammed Abdi Hashi (en) →
1 ga Augusta, 1998 - 8 ga Janairu, 2001 ← Office established (en) - Yusuf Haji Nur (en) → | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Galkayo (en) , 15 Disamba 1934 | ||||||
ƙasa | Somaliya | ||||||
Mutuwa | Abu Dhabi (birni), 23 ga Maris, 2012 | ||||||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon huhu) | ||||||
Ƴan uwa | |||||||
Abokiyar zama | Hawa Abdi Samatar (en) | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Somali National University (en) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Aikin soja | |||||||
Digiri |
colonel (en) lieutenant colonel (en) | ||||||
Ya faɗaci | Ogden War (en) | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Transitional Federal Government (en) | ||||||
An haifi Abdullahi Yusuf a ranar 15 ga watan Disamba shekara ta 1934 a Galkayo, wanda ke cikin yankin Mudug na arewa maso tsakiyar Somaliya . Birnin ya kasance a lokacin wani ɓangare na Somaliland na Italiya.[1] Iyalinsa sun fito ne daga dangin Omar Mahmoud na dangin Majeerteen Darod Harti Darod mafi girma.
yayi karatun sakandare, Ahmed ya yi karatun a fannin shari'a a Jami'ar Kasa ta Somalia da ke Mogadishu . Daga baya ya koma kasashen waje don ci gaba da karatun soja.[2] Ahmed ya sami takardar sheddar digiri a fannin Topography na Soja daga Kwalejin Soja ta M. V. Frunze a tsohuwar Tarayyar Soviet wata babbar cibiyar da aka tanada wa manyan jami'an sojojin Warsaw Pact da abokansu.[3][4] Ya sami ƙarin horo na soja a kasar Italiya.[3]
Ahmed ya auri Hawa Abdi Samatar . Ma'auratan suna da 'ya'ya maza guda biyu da mata biyu ban da jikoki shida.[5]
Ahmed ya shiga aiki Soja a kasar Somaliya a shekarar 1950. A shekara ta 1954 an haɗa shi a cikin rukunin farko na ma'aikatan soja na kasar Somaliya waɗanda aka kai su kasar Italiya don basu horar da Jami'ai. Rukunin sun hada da Aidid, Samatar, da Gabeyre. A Kara mashi girma zuwa mukamin kwamandan a shekara ta 1960. [6] A matsayinsa na soja, ya shiga cikin yakin shekara ta 1964 da aka yi da kasar Habasha kuma an yi masa ado saboda ya kasance babban jarumi .[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Index Ah-Al – Ahmed, Abdullahi Yusuf". Yobserver.com. Archived from the original on 10 February 2013. Retrieved 5 September 2013.
- ↑ New People Media Centre (Nairobi, Kenya), New people, Issues 94–105, (New People Media Centre: Comboni Missionaries, 2005).
- ↑ 3.0 3.1 "New president offers hope for war-torn Somalia". Yobserver.com. Archived from the original on 10 February 2013. Retrieved 5 September 2013..
- ↑ Ahmed III, Abdul. "Brothers in Arms Part I" (PDF). WardheerNews. Archived from the original (PDF) on 3 May 2012. Retrieved 28 February 2012.
- ↑ dalnuurshe01 says. "SOMALIA: Former Somalia president dies 87 (Brief History)". Raxanreeb.com. Archived from the original on 26 March 2012. Retrieved 5 September 2013.
- ↑ Janice Hamilton, Somalia in Pictures, (Twenty-First Century Books: 2007), p. 70.
- ↑ "Profile: Somali's newly resigned President Abdullahi Yusuf Ahmed". News.xinhuanet.com. 29 December 2008. Archived from the original on 1 January 2009. Retrieved 5 September 2013.