Jump to content

Abdulmumini M. Hassan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulmumini M. Hassan
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Jigawa South-West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Jigawa South-West
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Abdulmumini M. Hassan Zareku, ɗan siyasan Najeriya ne wanda aka zaɓa sanata mai wakiltar mazaɓar Jigawa ta Kudu maso yammacin jihar Jigawa, Najeriya a zaɓen tarayya na watan Afrilun shekara ta 2011. Ya yi takara a dandalin Jam’iyyar PDP.

Zareku ya kasance mataimakin shugaban jam'iyar PDP reshen jigawa ta tsakiya kuma kwamishinan da ke wakiltar jihar jigawa a hukumar halayen tarayya, lokacin da aka zabe shi a matsayin dan takarar PDP na kujerar sanatan Jigawa ta kudu maso yamma a zaben fidda gwani na PDP. Ya yi nasara da jimillar kuri'u guda 1,528 a zaben farko.

Zareku yana da kimanin shekara 50 lokacin da ya tsaya takara. Ya kuma samu kuri'u 212,322 a babban zaben Najeriya na watan Afrilu na shekarar 2011, gabanin babban abokin hamayyarsa Mallam Mujitaba Mohammed Mallam na jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) da kuri'u 89,718 da Ayuba Adamu Madaki na jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da kuri'u 69,324.[1][2] [3]

  1. ISMAILA MUHAMMAD (10 January 2011). "PDP's national vice chairman picks Senatorial seat in Jigawa". Daily Triumph. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 2011-05-06.
  2. "April 9, election results and updates". Daily Triumph. 15 April 2011. Retrieved 2011-05-06.[permanent dead link]
  3. "Collated Senate results". INEC. Archived from the original on 2011-04-19. Retrieved 2011-05-06.