Abdulrasheed Bawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulrasheed Bawa
Rayuwa
Haihuwa 30 ga Afirilu, 1980 (43 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Usmanu Danfodiyo
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara

Abdulrasheed Bawa (an haife shi a ranar 30 ga watan Afrilun 1980), ɗan Najeriya ne mai bincike kuma jami'in tilasta bin doka wanda a halin yanzu yake aiki a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Tu'annati wato (EFCC) tun a ranar 24 ga watan Fabrairun Na shekara ta 2021. Ya maye gurbin Umar Mohammed Abba, shugaban riko na hukumar.[1] Har zuwa lokacin da aka naɗa shi, ya kasance mataimakin babban Sufeto na hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa.[2][3] An naɗa Bawa a matsayin babban shugaban hukumar EFCC a ranar 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, a ranar 24 ga watan Fabrairu 2021 Majalisar Dokoki ta ƙasa ta tabbatar da shi a matsayin Shugaban Zartaswa a hukumance ya karɓi ragamar shugabantar hukumar[4][5] daga hannun Mista Ibrahim Magu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya a Hukumar.[6]

Rayuwar Farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abdulrasheed Bawa a shekarar 1980 kuma dan asalin garin Jega ne a jihar Kebbi.[7]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Ya samu takardar shaidar kammala karatunsa na farko a Makarantar Firamare ta zamani a Birnin-kebbi a shekarar 1991, sannan ya samu takardar shaidar kammala sakandare a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Owerri a cikin shekarar 1997. A shekarar 2001 Bawa ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, inda ya samu digiri na farko a fannin Kimiyya tttalin arziki[8] ya yi digirin-digirgir a fannin harkokin kada da ƙasa da diflomasiyya duk dai a jami'ar dan fodiyo a cikin shekarar 2012; kuma a halin yanzu yana karatun Bachelor of Laws a Jami'ar London.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Abdulrasheed Bawa ya fara aiki da hukumar EFCC ne a matsayin mataimakin Sufeto (ADS) a cikin shekarar 2004. A watan Oktoban shekarar 2015 aka nada shi ya jagoranci binciken Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur da mukarrabanta. Yana daga cikin tuhumar da aka yi mata zamba, cin hanci da rashawa a hukumance, zamba a banki, halasta kudaden haram da sauran laifuka masu alaka da cin amana. Kuma shi ne Shugaban hukumar EFCC mafi karancin shekaru[9]. Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (FINCEN) da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan sha da miyagun kwayoyi (UNODC) ne suka horar da shi.

Zargin da ake tuhumarsa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan seftamban shekara ta 2020, wani gidan jarida mai suna Peoples Gazette ya wallafa wani rahoto da ake zargin Bawa akan satar wasu motocin dake daukar man fetur kuma ya siyar dasu kuma duk da kasancewar shi shugaba a hukumar EFCC. Rahotan ya nuna cewa an kama Bawa kuma ya kasance na tsare na wasu kwanaki domin bincike a lokacin mai kula da hukumar ta EFCC na rikon kwarya wato Ibrahim Magu

Lokacin da aka gabatar da  Bawa a matsayin shugaban EFCC Bayan an cire Magu daga matsayin

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ade, Adesomoju (16 February 2021). "PROFILE: Abdulrasheed Bawa to make history as EFCC chairman". Premium Times. Retrieved 28 February 2021.
  2. "President Buhari don nominate new EFCC chairman". BBC News Pidgin. Retrieved 28 February 2021.
  3. Odutola, Abiola (24 February 2021). "Meet the new EFCC Chairman, Abdulrasheed Bawa". Nairametrics. Retrieved 28 February 2021.
  4. "Nigerians to have access to information on EFCC operations — Abdulrasheed Bawa". Vanguard News. Vanguards News. 24 February 2021. Retrieved 28 February 2021.
  5. Dennis, Erezi. "Senate confirms 40-year-old Bawa as EFCC chairman". guardian.ng. Guardian News. Retrieved 28 February 2021.
  6. "Without police background, Bawa becomes EFCC boss". Retrieved 5 May 2021.
  7. Ade, Adesomoju (16 February 2021). "PROFILE: Abdulrasheed Bawa to make history as EFCC chairman". Premium Times. Retrieved 28 February 2021.
  8. Ade, Adesomoju (16 February 2021). "PROFILE: Abdulrasheed Bawa to make history as EFCC chairman". Premium Times. Retrieved 28 February 2021.
  9. Ade, Adesomoju (16 February 2021). "PROFILE: Abdulrasheed Bawa to make history as EFCC chairman". Premium Times. Retrieved 28 February 2021.